By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Najeriya ta Halarci Taron Kasashan Musulmai na Duniya Domin Tabbatar da Tsagaita Wuta a Gabas ta Tsakiya da Kuma Tabbatar da Kasashe Gaza da Isra’ila.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Najeriya ta Halarci Taron Kasashan Musulmai na Duniya Domin Tabbatar da Tsagaita Wuta a Gabas ta Tsakiya da Kuma Tabbatar da Kasashe Gaza da Isra’ila.
International News

Najeriya ta Halarci Taron Kasashan Musulmai na Duniya Domin Tabbatar da Tsagaita Wuta a Gabas ta Tsakiya da Kuma Tabbatar da Kasashe Gaza da Isra’ila.

Attajdid
Last updated: 2024/11/12 at 6:07 AM
Attajdid Published November 12, 2024
Share
SHARE

Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Musulmi da Larabawa.

Taron wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya.

Tinubu ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin matamakin gwamnan Riyadh, Mohammed Abdurrahman.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra’ila da Falasɗinawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar tsagaita wuta nan take, tare da neman a sake farfaɗo da masalahar samar da ƙasashe biyu masu cin gasin kansu wato Falasɗinu da Isra’ila.

Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya ce Najeriya ta halarci taron ne sabo da irin daɗaɗɗiyar alaƙa mai kyau da take da ita da yankin na Gabas ta Tsakiya.

“Dole ne mu samar da hanyar diflomasiyya domin warware wannan rikicin, saboda yaƙi ba shi ne mafita ba,” kamar yadda ministan ya faɗa wa manema labarai a birnin Riyadh. “Wannan shi muke buƙata a yi.”

Ya ce Najeriya za ta kuma yi amfani da lokacin taron wajen nema “da babbar murya a idon duniya” buƙatar dukkan ƙasashe su cimma matsaya ɗaya ta warware rikicin Isra’ila da Falasɗinu.

“Ƙasashen biyu da ke rikici da juna na rasa abubuwa muhimmai, don haka Najeriya na ganin cewa muddin ba a samar da mafita ta diflomasiyya ba, rikicin zai iya shafar ɗaukacin yankin, har ma da duniya baki ɗaya.

“Babu yadda Najeriya za ta zauna cikin kwanciyar hankali muddin ba a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba,” in ji Idris.

Harin da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya janyo mutuwar mutum aƙalla 1,200, da kuma yin garkuwa da kusan 251.

Tun bayan nan, Isra’ila ta kaddamar da mamaya kan zirin na Gaza, inda ta kashe sama da mutum 43,000, waɗanda yawancinsu mata ne da kuma ƙananan yara.

Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da farmaki a Gaza har sai ta ga bayan ƙungiyar Hamas da ke iko a Gaza.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 12, 2024 November 12, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Yahudawan Sahyoniyya Sun Kashe Saban Shugaban Hezbollah

Attajdid Attajdid October 25, 2024
Atiku ya Gargaɗi Tinubu Akan Yawan Ciyo Bashi
Without astronauts, Boeing’s Starliner Returns to Earth
Child Birth Spacing Key To Improve MNCH
Amurka Ta ƙaƙabawa Editocin Gidan Talabijin ɗin RT Na Rasha Takunkumai
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?