By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Zaftarewar ƙasa a Kamaru ta kashe aƙalla mutum 12
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Zaftarewar ƙasa a Kamaru ta kashe aƙalla mutum 12
International News

Zaftarewar ƙasa a Kamaru ta kashe aƙalla mutum 12

Attajdid
Last updated: 2024/11/10 at 12:22 PM
Attajdid Published November 10, 2024
Share
SHARE

Har yanzu akwai gomman mutane da ba a gansu ba, inda ake ci gaba da neman su, kamar yadda hukumomi a ƙasar suka tabbatar

 

Ma’aikatan bayar da agaji sun gano gawawwaki 12 sakamakon wata zaftarewar ƙasa da ta faru a yammacin Kamaru, kamar yadda wani jami’in yanki ya bayyana a ranar Asabar, inda ya ƙara da cewa babu tabbacin gano wasu masu rai.

 

Kafar watsa labarai ta ƙasar CRTV ta ruwaito gwamnan yankin Ouest, Augustine Awa Fonka, yana tofa albarkacin bakinsa dangane da lamarin.

 

“A ganinmu, ba mu tunanin akwai yiwuwar a sake gano wani mai rai,” kamar yadda ya shaida wa kafar watsa labaran.

 

An gano gawawwaki 12 daga wurin da lamarin ya faru, mutum na ƙarshe shi ne a ranar Asabar, in ji shi.

 

Ana ci gaba da nema

 

Har yanzu akwai gomman mutane da ba a gansu ba, inda ake ci gaba da neman gawawwakinsu, kamar yadda ya ƙara da cewa.

 

Zaftarewar ƙasa biyu ta faru a saman wani tsauni a ranar Talata – ta biyun a daidai lokacin da ma’aikatan bayar da agaji ke amfani da manyan kayayyakin aiki domin gyara hanya.

 

Ƙasar ta zaftare da manyan motoci uku masu ɗaukar mutum 20, da motoci masu ɗaukar mutum biyar da babura da dama, kamar yadda Awa Fonka ya bayyana a sanarwarsa ta baya.

 

Hanyoyin kasar Kamaru suna da hatsarin gaske, inda kusan mutane 3,000 ke mutuwa a kowace shekara a sanadiyyar hadurra, ko kuma sama da mutum 10 daga cikin mazaunan 100,000, a cewar sabbin alkalumman Hukumar Lafiya ta Duniya, da aka buga a shekarar 2023.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 10, 2024 November 10, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Mother Of Seven Join Campaigns For Family Planing In Jigawa  

Attajdid Attajdid December 14, 2024
16 died, 3,936 Displaced By Flood In Jigawa.
December 12, 2024
PRESS CONFERENCE ON BEHALF OF THE COMMISSIONER OF POLICE, KANO STATE COMMAND, CP SALMAN DOGO GARBA BY SP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA, PPRO, ON RELENTLESS EFFORTS OF THE COMMAND IN THE FIGHT AGAINST CRIME AND CRIMINALITY IN THE STATE, HELD ON 2ND SEPTEMBER 2024 AT THE STATE HEADQUARTERS IN BOMPAI KANO
Da Yuwar Wahalar Fetur Zata Kara Ta’azzara a Nigeria
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?