Aƙalla ƙarin sojojin Isra’ila 23 sun sami raunuka a arangamar da aka yi a Gaza da kuma kudancin Lebanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Alkaluman sojin Isra’ila sun nuna cewa shida daga cikin sojojin sun jikkata a Gaza, ba tare da bayyana inda sauran sojojin suka jikkata ba.
Alkaluman sun ce akalla sojoji 749 ne aka kashe yayin da wasu 5,018 suka jikkata tun bayan barkewar rikicin Gaza a ranar 7 ga Oktoban 2023.
At-tajdid News.




