By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ga dukkan alamu za a gwabza yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran — Fidan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Ga dukkan alamu za a gwabza yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran — Fidan
International News

Ga dukkan alamu za a gwabza yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran — Fidan

Attajdid
Last updated: 2024/10/19 at 9:08 PM
Attajdid Published October 19, 2024
Share
SHARE

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi gargaɗi da cewa dole Turkiyya da ma yankinsu su shirya fuskantar yaƙin da za a iya gwabzawa tsakanin Isra’ila da Iran saboda “akwai yiwuwar hakan ta faru matuƙa”.

 

“Dole ne a kalli yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran a matsayin abu da zai iya yiwuwa sosai,” in ji Fidan a wata tattaunawa a tashar talabijin a ranar Alhamis.

 

Ya ƙara da cewa “Na yi amanna cewar wannan lamari zai iya faruwa kuma matakin farko da ƙasashen yankin za su ɗauka shi ne su shirya tunkarar wannan yanayi, a matsayin ƙasa da kuma yanki. Wannan ba abu ne da muke buƙatar ya yaɗu ba. Yaɗuwar yaƙi da tayar da tarzoma a yankin ba su ne abin da muke son gani ko fata ba.”

 

Turkiyya ba ta goyon bayan “duk wani rikici da za a yi da Iran wanda zai rikiɗe ya koma yaƙi,” Ankara na adawa da hakan, inda ya yi tsokaci da cewar Tehran na da haƙƙin kare kanta.

 

Da yake bayani kan manufofin Turkiyya na ƙasashen waje da harkokin tsaro, Fidan ya ce Turkiyya “ba ta sanya idanuwanta a kan ko da taƙi ɗaya na ƙasar wani ba, kuma tana son ƙulla alaƙa ta ci-gaban yankin da zaman lafiya da walwala.”

 

Fidan ya yi nuni da cewar adawar da ke tsakanin China da Amurka za ta ƙara ƙamari, yana mai nuni da gogayyar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.

 

‘Buɗaɗɗiyar maƙabarta’

 

Game da iƙirarin mutuwar shugaban ɓangaren siyasa na Hamas Yahya Sinwar, Fidan ya ce Ankara na jiran tabbatar da hakan daga Hamas, yana mai ƙarawa da cewar babu wani labarin musanta hakan da suka samu.

 

“Abin takaici Gaza ta zama buɗaɗɗiyar maƙabarta inda ake kashe dubban waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, ana aikata kisan kiyashi,” in ji shi.

 

Ya yi tsokaci da cewar Ankara ta auna ta ga yadda Isra’ila “ta shirya ɗaukar matakin soji na ɗaya bayan ɗaya ta kawar da duk wani da ya fuskance ta, ciki har da Hamas, Hezbollah, Houthi da ke Yemen, da sauransu,” ya kuma bayyana fatan Turkiyya na hana yiwuwar buɗe sabon babi na yaƙin.

 

Da yake bayyana yadda sauran ƙasashen yankin ba sa nuna wa Lebanon irin damuwar da suke nuna wa Falasɗinawa, Fidan ya ce “Akwai dalili a nan. Wannan dalili shi ne, tabbas mai girma da ma’ana. Muna buƙatar kallon dalilan da suka janyo hakan.” TRT Afarka Hausa.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 19, 2024 October 19, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Yahudawan sahyoniyya na Isra’ila Sun Kai Hari Wata Makaranta a Gaza da ya yi Sandiyar Mutuwar Mutane 22

Attajdid Attajdid October 14, 2024
Kasashen Afirka da suka fi cin bashin Asusun Lamuni na Duniya (IMF)
ASUU Faults University”s Administrators, Governing Boards on Abuse Of Power
Isra’ila Ta Cigaba Da Ruwa Bama-bamai Kan Fararen hula A Gaza
Burkina Faso da Senegal za su ƙulla alaƙar tsaro
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?