Isra’ila ta kai wasu hare-hare ta sama a kudanci da gabashin Lebanon da kudancin Beirut da ke zama tungar ‘yan Hezbollah. Amma kungiyar ta dauki fansa inda ta harba makamai 85 a birnin Haifa da ke arewacin Isra’ila.
Firayiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga ‘yan Lebanon da su ceto kasarsu daga hannun kungiyar Hezbollah, ko kuma sun fuskanci farmakin da zai haifar da wahala kamar yadda ya wakana a Gaza. A cikin wani sakon bidiyo da aka watsa cikin harshen Ingilishi, Netanyahu ya yi barazanar ganin bayan shugabannin Hezbollah, inda ya ce dakarunsa sun kawar Hassan Nasrallah tsohon shugaban Hezbollah da wanda ya maye gurbin Nasrallah da jagoran baya-bayannan nan da aka zaba, amma ba tare da bayyana sunansa ba.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




