Akalla sojojin Isra’ila 48 ne suka jikkata a Gaza da Lebanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda shafin intanet na rundunar sojojin Isra’ila ya bayyana.
Isra’ila ta zafafa kai hare-hare ta kasa a gabar tekun kudancin Lebanon, inda ta tura karin sojoji tare da yin kira ga fararen hula da ke kusa da Tekun Bahar Rum da su ƙaurace wa gidajensu.
Kungiyar Hezbollah ta ce ta harba makami mai linzami a birnin Haifa na Isra’ila bayan da sojojin Isra’ila suka bayar da rahoton cewa an harba makamai 85 daga Lebanon.
Yaƙin da Isra’ila ta kwashe shekara guda tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,870. Kazalika, Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon tun Oktoban 2023 inda ta kashe fiye da mutum 2,000, ta raba fiye da mutum miliyan 1.2 da muhallansu.TRT Afarka Hausa.
At-tajdid News.




