Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta NECO, ta ce kaso 60% na daliban da suka rubuta jarrabawar NECO sun ci darussa 5 zuwa sama ciki har da Lissafi da Turanci a sakamakon da aka fitar.
Shugaban hukumar, farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya sanar da haka, a lokacin da yake bayani game da jarrabawar da kuma irin sakamakon da aka samu.
leadership.ng.
Mai rahoto;
Zainab Sulaiman.
At-tajdid News.




