Dakarun Al-Qassam sun kai hari kan wani babban soji na D9 da harsashi Al-Yassin 105 a gabashin unguwar Al-Tanour da ke birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza shaidu da Mujahidan sun tabbatar da kwace wata motar soji mai dauke da jirage marasa matuka a yankin kamar yadda majiyarmu ta yankin ta shedawa At-tajdid News.
Kamar yadda Al-jazeera ta kawo an sami shahidai da dama a harin bam da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar Al-Zaytoun da ke birnin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun lalata wurare kusan 180 da dubunnan makaman roka a kudancin Labanon daga basani kuma an sami rahotan harba makaman roka a wasu yankuna a kudancin Labanon dakarun Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare kan ababen more rayuwa na Hizbullah tare da kwace ikonsu.
Al Jazeera.Rikicin kungiyar Hizbullah yana tattare da makiya Isra’ila yin haka bai zama wani sabon abu gare ta ba musamman shugabanninta da daidaikun mutane da masu saurarenta.
Ma’aikatar kula da lafiya na kasar Labanon ya bada rahotan kashe mutane 37 sakamakon harin bam da aka kai a kudancin birnin Beirut, kuma ana ci gaba da aikin kwashe baraguzan ginin.
Jagoran kungiyar Ansar Allah, Abdul-Malik Al-Houthi ya bayyana irin gudunmawar da Hizbullah ta bada wajen korar dubban daruruwan ‘yan kama-wuri-zauna a mazaunan da suke arewacin Falasdinu.
At-tajdid News.




