By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Akalla An Sami Mutane 30 Sun Mutu a Ambaliyar Ruwan data Barke a Jahar Maiduguri.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Akalla An Sami Mutane 30 Sun Mutu a Ambaliyar Ruwan data Barke a Jahar Maiduguri.
News

Akalla An Sami Mutane 30 Sun Mutu a Ambaliyar Ruwan data Barke a Jahar Maiduguri.

Attajdid
Last updated: 2024/09/12 at 9:32 AM
Attajdid Published September 12, 2024
Share
SHARE

Rundunar sojin Nijeriya da ‘yan sa kai da sauran hukumomin tsaro suna ci gaba da aikin ceton mutanen da suka maƙale a cikin ambaliyar ruwa suna kai su wuraren da ke da aminci.Mummunar ambaliyar ta yi sanadin aƙalla rayukan mutum 30 da kuma raba mutum 400,000 da muhallansu, kamar yadda jami’ai suka faɗa a ranar Laraba.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Ezekiel Manzo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “Mutum 30 ne suka mutum.”

Ita ma shugabar hukumar NEMA Zubaida Umar ta ce “Al’amarin Maiduguri yana da ban tsoro.”

“Ambaliya ta mamaye kusan kashi 40 cikin 100 na daukacin birnin, an tilasta wa mutane barin gidajensu kuma sun bazu ko ina.Da ya ziyarci yankunan da lamarin ya fi ƙamari a Maiduguri, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya zagaya yankin unguwar Custom inda gidan yarin yake.

Yayin da ake rangadin, ana kwashe gawarwakin mutane. Hakazalika sojoji da jami’an tsaro da masu aikin sa kai na farar hula suna kwashe mutanen da suka maƙale.

Duk da cewa ruwan ya fara janyewa a wasu wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye a Maiduguri, yankunan da abin ya fi ƙamari kamar su Kasuwar Gamboru da Kasuwan Shanu da Custom Area da Fori, da Abbaganaram har yanzu a malale suke.

La’akari da yanayin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a Nigeria wannan ambaliyar ruwa da ake ta samu a wasu sassan kasarnan na iya haifar wasu matsaloli daban da kuma yiwa barkewar annoba matikar gwamnatoci basu dauki matakan da ya kamata ba.A daya hannin kuma ana cigaba da aikin ceto kamar yadda hukumar NEMA ta bayyana  sama da gidaje 23,000, da mutum 150,000 ne suka fuskanci bala’in ambaliyar ruwan.

Mun kuma aike da dakunan shan magani na tafi da gidanka da kayayyakin jinya tare da likitocin asibitin sojoji domin kula da ‘yan gudun hijirar da ke sansanoni da ke bukatar kula da lafiya,” in ji Zubaida.“

Hakan yana da muhimmanci domin babban asibitin Maiduguri shi ma ambaliyar ya shafe shi.

Mun samar da kwale-kwale da masunta da ke shiga cikin al’ummomin da ambaliyar ruwa ta mamaye tare da kubutar da mutanen da suka makale.”Ta kara da cewa, “Mun tura tankunan mu na ruwa domin samar da ruwan sha mai tsafta saboda mun damu da yiwuwar barkewar cututtuka masu yaduwa.

”At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid September 12, 2024 September 12, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa AFAN Hails Supreme Court Judgment Upholding Dr. Mudi as National President 

Attajdid Attajdid August 9, 2025
Tallafin Kanyan Amfani da Aka Kaiwa Wadanda Ambaliyar Ruwan Maiduguri ta Shafa Daga Kungiyar Jama’atut Tajdidil Islamy (JTI)
WANENE JABOTINSKY WANDA NETANYAHU YAKE BI  KUMA YA AJIYE TAKOBINSA?(ko kasan Banjamin Netenyahu da manufofinsa?)
Isra’ila Na Amfani Da Daimon ɗin Afirka Don Tallafawa Kisan ƙare Nangi a Gaza.
Bikin Cika Shekaru 101 da Zama Jamhuriyar Kasar Turkiyya
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?