Daraktan ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya bayyana irin takurar da dakarun Isra’ila ke yi a Gaza a tsawon kwanaki 100, dakarun sun hana shigar da manyan motocin agaji zuwa yankin hakan ya biyo bayan takaddamar da sojojin suke yi na shigar da kayan agaji, hakan ya kara matsananciyar yunwa a zirin Gaza a cikin kwanaki 100 da suka gabata ta yadda suke cigaba da mamayar wuraran paledinawa da kuma kokarin hana shigar da dukkan kayayyakin jinya yankin Gaza dakarun Isra’ila sun lalata tsarin kiwon lafiya tare da hana marasa lafiya feye da 25,000 fita kasashen waje don naiman magani daraktan ofishin lafiya na Gaza ya yi Allah wadai da ci gaba da rufe iyakar Rafah tsakanin Falasdinu da Masar haka zalika Sama da yara dubu dayane (1000) marasa lafiya suka mutu cikin kwanaki 100.
Suna daukan matakan hana marasa lafiya fita kasashan waje don yin jinyar ya kara da cewa “Muna neman a bude mashigar Rafah domin kawo agaji tare da bayar da damar kai marasa lafiya zuwa kasashen waje kuma Muna kira ga kasashen duniya da su matsawa Isra’ila lamba don dakatar da yakin da ake yi a Gaza.
At-tajdid News.




