Majiyoyin kiwon lafiya na Al Jazeera yace an sami Shahidai 25 a ci gaba da kai hare-haren bam da Isra’ila ke kaiwa Zirin Gaza tun da safiyar yau, 18 daga cikinsu a Khan Yunis suke.

Dakarun Quds Tare da Al-Qassam sun lalata tankar yahudawan Sahayoniya ta Merkava 4 Baz tare da wani babban bama-bamai a unguwar Tal Al-Sultan da ke yammacin Rafah dake Gaza.

Ma’aikatar Lafiya a Gaza ta bayyana adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa shahidai 39,897 da kuma jikkata 92,152 tun daga ranar 7 ga Oktoba.
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




