Ma’aikatar lafiya ta jihar Borno ta ayyana ɓarkewar annobar kwalara a faɗin jihar, inda aka fargabar fiye da mutum 450 sun kamu amma an tabbatar da kamuwar mutum 17 kawo yanzu.
Kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Baba Gana ne ya bayyana hakan lokacin da yake ayyana ɓarkewar annobar, inda ya ce daga cikin gwaji fiye da 200 da aka yi, 17 sun kamu da cutar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ɓarkewar cutar dai ya faru ne sakamakon annobar ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita ɗaruruwan ƴan jihar.
Farfesa Baba Gana ya ce an samu ɓarkewar cutar a ƙananan hukumomin Jere da Mafa da Konduga da Dikwa da Ƙaramar Hukumar birnin da kewaye.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu.
At-tajdid News.




