WACECE JANNA JIHAD ❓
(جنى جهاد عياد التميمي)
AAE²/061/2024
An haifi Janna Jihad Ayyad Al-Tamimi a 6 ga watan Afrilu 2006, ta kasance yar gwagwarmaya Falasdinu ce kuma yar jarida mai yin rubutu a shafuffukan ta na sada zumunta na Facebook da Twitter
Ta fara ba da rahoto game da rikicin Isra’ila da Falasdinu tun tana da shekaru bakwai a duniya bayan an kashe wasu yan uwanta biyu, sannan tana daya daga cikin ƴan jarida masu mafi karancin shekaru a duniya, wanda har ana mata laƙani da (The youngest journalists in the world)
Tun da farko JANNA ta fara amfani da wayar hannun mahaifiyarta don ɗaukar bidiyon zanga-zangar da ake yi a kusa da gidan su tare da dora su zuwa kafafen sada zumunta na zamani Irin su Facebook, Instagram, Snapchat, da YouTube, zuwa yanzu dai JANNA Tana da mabiya sama da 620,000 a Facebook.

Sannan kuma ta na ba da labarin abubuwan da suke faruwa a Jerusalem da Jordan da yaren Larabci da Turanci
A cikin watan Maris ɗin 2017 JANNA ta sami lambar yabo ta kasa da kasa a Istanbul, kasar Turkiyya, an nuna ta a cikin shirin Radiance of Resistance lokacin tana da shekara tara, an kuma yaba mata a matsayin ‘yar jarida mai fafutuka a mafi ƙarancin shekaru.
Kalmar da JANNA take yawan faɗi itace “My camera is my GUN” wato kyamara ta itace makami na.
✍️ Zaharaddeen Zarumee Gusau.




