Majalisar Ɗinkin Duniya:
Kakakin Isra’ila a MDD ya ce: “Ba mu kan tsara matakanmu bisa ga bukatun Amurka koyaushe ba. Wani lokaci muna sanar da Washington kafin mu dauki mataki, wani lokaci kuma a lokacin aiwatarwa – a ƙarshe mu kan ɗauki alhakin abin da muka yi.”
Estonia:
Ministan Harkokin Wajen ƙasar ya bayyana matuƙar damuwa kan harin da Isra’ila ta kai a Doha, yana mai kiran shi take hakkin ƙasar Katar da kuma mataki da zai iya tayar da ƙarin rikici. Ya kara da cewa, “Katar tana taka muhimmiyar rawa wajen kokarin kulla tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin fursunoni, kuma muna goyon bayan hakan baki ɗaya.”
Qatar:
Firayim Minista kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar ya jaddada cewa ƙasarsu ba za ta lamunci take hakkin ikonta ba, tare da gargadin cewa za su ɗauki matakin da ya dace kan duk wani kutse na tsaron ƙasar.
Asibitin Shahidan Aqsa, Deir al-Balah:
Likitoci sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a sakamakon harin jirgin yaki marar matuki na Isra’ila da ya kai kan tantar ’yan gudun hijira a tsakiyar zirin Gaza.
Isra’ila:
Mahaifiyar ɗan Isra’ila da ke hannun Hamas, Elkana Buhbut, ta bayyana cewa damuwarta tana ƙaruwa tare da rasa fata a kullum game da dawowar ɗanta.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




