Rudunar Yansanda Ta Yi Gargadi Ga Yansiyasa Da ke Kalaman Tunzura Jamaa A Jihar Kebbi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta alakanta yawan samun rikicin da ake a tsakanin magoya bayan yan siyasa harma da yan siyasar kansu da yawan samun kalaman tinziri da akeyin daga jagororin siyasa a jihar., inda ta yi gargadi daukar tsattsauran mataki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sani Bello ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Birnin Kebbi a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da ta yi da gwamna Nasir Idris.
Ganawar ta biyo bayan harin da aka kai da safiyar yau kan ayarin motocin shugaban jam’iyyar (ADC) wato African Democratic Congress a jihar Kebbi da kuma tsohon ministan shari’a Abubakar Malami.
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bangar siyasa ne suka kai wa Malami hari a Birnin Kebbi a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da gamayyar jam’iyyar ADC a jihar Sakkwato ta samu gagarumin ci gaba bayan ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress, jim kadan bayan ya dawo jihar a ziyarar jaje.




