Gwamnatin Tarayya Zata Sabunta Tsarin Koyarawa A Makarantu Da, Jami’oi
Gwamnatin Tarayya ta kammala cikakken bitar manhajar makarantu na matakin firamare, sakandire da kuma na makarantun koyar da ilimin sana’o’i domin dora ɗaliban Najeriya a kan shirin da zai zamo daidai da buƙatunsu na gaba.
A cikin sanarwar da ma’aikatar ilimi ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Boriowo Folasade, da ya sanya wa takardar hannu a ranar Juma’a, aka kuma rabawa manema labarai.
Folasade ya ce karamar ministan ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ce ta sanar da manhajar a madadin ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, yayin da take jawabi a birnin Abuja.
A cewar ministar, an gudanar da wannan bita ne tare da haɗin gwiwar manyan masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, ciki har da hukumar bincike da ci gaban ilimi ta Najeriya NERDC da hukumar ilimin bai daya UBEC da hukumar ilimin Sakandire ta ƙasa NSSEC da kuma hukumar ilimin fasaha NBTE.
Sabon tsarin manhajar an tsara shi ne domin rage cunkoson a harkokin koyo da koyarwa, inganta sakamakon koyon ilimi, tare da tabbatar da cewa ɗaliban Najeriya suna samun ƙwarewar da ta dace da bukatun duniya na zamani.
Ƙarkashin sabon tsarin, ɗaliban aji daya zuwa 3 na Firamare za su yi karatu da darussa mafi ƙanƙanta daga 9 zuwa 10; yayin da ɗaliban aji 4 zuwa 6 na Firamare za su ɗauki darussa 10 zuwa 12.
Su kuwa ɗaliban karamar Sakandire za su ɗauki darussa 12 ne zuwa 14, sai kuma ɗaliban babbar Sakandire da za su yi darussa 8 zuwa 9, sannan ɗaliban makarantu na fasaha za su ɗauki darussa 9 zuwa 11.
Ma’aikatar ba ta bayyana takamaiman ranar da za a fara amfani da sabbin manhajojin ba, amma ta ce za a gabatar da su a hankali tare da kulawa daga hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da an aiwatar da su yadda ya kamata.




