NETANYAHU YA KUDURI ANIYAR CIGABA DA OPERATION GIDEON
Jaridar Maariv ta rawaito daga majiyoyin tsaro na Isra’ila:
Firaiminista Netanyahu ba shi da niyyar dakatar da aikin Operation Gideon’s Chariots 2.
Rahoton ya nuna cewa Netanyahu ya kuduri aniyar ci gaba da aikin har zuwa ƙarshe.
An ce ya fahimci cewa ba tare da wannan aiki ba, gwamnatin sa zata iya rugujewa.
Rundunar sojin Isra’ila ta kiyasta cewa yaki a Gaza na iya ci gaba na watanni masu yawa, don haka za a kira dakaru ajin ajiya a hankali.
✍️ Rahoto daga Mustapha Garba Usman




