By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Duk Basaraken Da Ya Daki Matarsa A Bakin Rawaninsa– Sarki Sanusi
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Duk Basaraken Da Ya Daki Matarsa A Bakin Rawaninsa– Sarki Sanusi
News

Duk Basaraken Da Ya Daki Matarsa A Bakin Rawaninsa– Sarki Sanusi

Attajdid
Last updated: 2025/07/22 at 12:28 PM
Attajdid Published July 22, 2025
Share
SHARE

Mai Martaba Sarkin Kano,Malam Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa matuka kan yadda ake kara samun karuwar cin zarafin mata da fyade a jihar Kano, inda ya bukaci hukunci mai tsauri kan masu aikata wannan mummunar dabi’a tare da jaddada cewa addinin Musulunci ba ya amincewa da dukan mace.

 

Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa a ranar Litinin, 21 ga Yuli, yayin da ya karɓi bakuncin wakilan cibiyar bunkasa bincike kan cigaban mata da cibiyar wayar da kai da shiga tsakani a mahangar addinin musulunci na Jami’ar Bayero, Kano.

 

“Ni ban taɓa yarda da dukan mace ba, kuma masu dukanta ba su yin hakan don gyara halayenta,” in ji Sarkin. “Abin da muke gani a yau shi ne duka mai tsanani da raunata mata da sunan gyara.”

 

Ya ci gaba da cewa: “Addinin Musulunci shi ne ya fi kowa girmama mace. Wanda ke dukar matarsa har ya ji mata rauni ba mutumin kirki ba ne. Ba ni na faɗa ba—Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ne ya faɗa. Wadanda ba sa karatu su ne ba su san haka ba.”

 

Sanusi ya jaddada cewa malamai da limamai na da rawar gani sosai wajen dakile wannan matsala a cikin al’umma, inda ya bukaci su rika amfani da mimbarori wajen ilmantar da mutane game da darajar mata a cikin Musulunci.

 

Ziyarar da DRPC da CICID suka kai fadarsa na cikin wani shiri da Ford Foundation ke daukar nauyi, wanda ke neman horar da shugabannin ra’ayi a cikin Musulmai domin yaki da cin zarafin mata a arewacin Najeriya.

 

Sarkin ya yaba da shirin, yana mai cewa ya zo a kan gaba kuma ya dace da lokaci. Ya bukaci kungiyoyin da su taimaka wajen farfado da Dokar Iyali ta Jihar Kano wadda, a cewarsa, na dauke da muhimman matakan shari’a da za su kare mata da iyalai daga cin zarafi.

 

“Dukkan dokokin da ake bukata tuni suna cikin littattafan fikhu na Musulunci. Abin da ya rage shi ne a tara su a dunkule su a matsayin tsari daya da za a iya amfani da shi,” in ji Sarkin.

 

Yayin da ya ke tunawa da binciken da ya gudanar a matsayin dalibi, Sarkin ya bayyana cewa kundin digirinsa na digiri na uku (PhD) ya mayar da hankali ne kan tsara dokokin iyali na Musulunci, inda ya yi nazari kan kotunan Shari’a tara a Kano na tsawon shekaru biyar. Sakamakon binciken ya nuna yadda ake yawan cin zarafin mata a fadin jihar.

 

A karshe, Sarkin ya ja kunnen shugabannin gargajiya, yana mai cewa: “Na umurci dukkan dagatai da hakimai cewa duk wanda aka samu da laifin dukan matarsa zai rasa sarautar gargajiyarsa.

 

Mai rahoto;

Salihu Garba

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid July 22, 2025 July 22, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Gwamnatin Nijar ta Dakatar da Watsa Shirye-Shiryen BBC a ƙasar

Attajdid Attajdid December 13, 2024
Jigawa Speaker Calls for Global Action on Girls’ Education, Security, and Safety
Governor Radda Call For Prayer Against Insecurity In Nigeria
Amurka Ta ƙaƙabawa Editocin Gidan Talabijin ɗin RT Na Rasha Takunkumai
Dakarun Qassam Sun Kwace wata Mota Dauke Da Jirgi mara Matuki Yayin Da Isra’ila take Lugudan Wuta a Lebanon
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?