Ministan harkokin wajen Iran Ya Magantu Akan Tattaunawa da Amurka
Amurka na son tattaunawa kuma ta aike da sakwanni masu mahimmanci dangane da hakan.
Mun tabbatar wa Amurka cewa ba zai yiwu a yi magana game da shawarwarin ba yayin da ake ci gaba da ta’addanci.
Kuma muna kokari kare kan mu da kuma Kare ƙasarmu daga zalunci, kuma ba za a tattaunawa da Amurka ba kamar yadda ta zama abokiyar tarayya a cikin waɗannan laifuka. Ba za mu tuntuɓe ta ba a halin da ake ciki yanzu.
Babu wani batun tattaunawa da wata kungiya game da karfin makamanmu na makami mai linzami, kuma kowa ya san cewa suna kare filayenmu ne. (Aljazeera)
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




