Jami’ai a Afghanistan sun ce aƙalla mutum huɗu sun jikkata bayan harin gurneti a wani masallaci a lardin Samangan da ke arewacin ƙasar.
Hukumomin ƙasar sun ce lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a birnin Aybak.
Ƴansanda sun kama mutum biyu da suke zargi da hannu a lamarin.
Lamarin na zuwa ne a kwana guda bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum guda tare da raunata wasu uku a cikin harabar ma’aikatar raya birane da ke birnin Kabul. BBC Hausa.
Asalin hoton,Getty Images
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




