Raila Odinga ya ce bai kamata a kakaba wa al ummar Africa shiga sahun abinda babu sa hannunsu aciki.
Tsohon firaministan Kenya Raila Odinga ya ce bai kamata a kakaba wa al’ummar Afirka shiga sahun warware matsalar sauyin yanayin da babu hannunsu wajen samar da ita ba.”
Ya fadi hakan ne a wajen bikin kaddamar da shi a matsayin dan takarar Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka daga Kenya da aka yi a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha a ranar Juma’a 8 ga watan Nuwamba.
Kenya ta gabatar da tsohon Firaminista Raila Odinga a matsayin “cikakken ƙunshi” don maye gurbin shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat.
Faki mai shekaru 64 zai bar mulki bayan zaben hukumar AU a watan Fabrairun 2025.
Mai Rahoto.
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




