By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Shugaba Paul Biya ya Koma Kamaru Bayan Shafe Makonni ba ya nan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Shugaba Paul Biya ya Koma Kamaru Bayan Shafe Makonni ba ya nan
International News

Shugaba Paul Biya ya Koma Kamaru Bayan Shafe Makonni ba ya nan

Attajdid
Last updated: 2024/10/22 at 9:30 PM
Attajdid Published October 22, 2024
Share
SHARE

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sauka a babban filin jiragen sama na Yaounde a ranar Litinin, bayan da ya shafe makwanni da barin kasar, inda aka yi ta jita-jita game da lafiyarsa, kamar yadda gidan talabijin na kasar CRTV ya nuna.

 

An nuna shugaban kasar mai shekara 91 a gidan talabijin a lokacin da yake sauka daga jirgi, inda ya dinga musabaha da jami’an da ke kusa da matarsa Chantal, a daidai lokacin da jama’a ke ta murna suna jiran tarbarsa.

 

Magoya bayansa da suke jeru a titi sun yi ta buga ganguna da rera waƙoƙi ɗauke da hotunansa, a lokacin da shugaban ke wucewa don tafiya fadarsa, kamar yadda kafar yada labarai ta CRTV ta bayyana, a yayin da take watsa yadda saukar tasa ta kasance.

 

An yi ta kokwanto kan halin lafiyar Biya da kuma inda ya tafi bayan da aka daina jin ɗuriyarsa tun bayan taron da ya halarta na ƙasashen Afirka da China a birnin Beijing a watan Satumba.

 

Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na CRTV ya ce “A yau shugaban kasa na kan hanyarsa ta dawowa, kuma hakan zai kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa.”

 

Shafin da ke bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama ya nuna jirgi ƙirar Boeing mai lamba CMR001, wanda shi ne Biya ke hawa, ya bar birnin Geneva na Switzerland a ranar Litinin, inda a can shugaban yake tsawon makonni, in ji majiyoyin hukuma.

 

An mammanna manyan fastocin shugaban ƙasar wanda ya shafe shekara 40 yana mulki ba hamayya a babban birnin kasar ana yi masa maraba gabanin komawar tasa.

 

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wajen ya ce an rubuta a ɗaya daga cikin allunan cewa “Barka da dawowa gida, Shugaban Kasa.”

 

A ranar 8 ga watan Oktoba ne gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwa bayan da aka yi ta yaɗa jita-jita, inda ta ce Shugaban Ƙasar ya kusa komawa gida.

 

Sannan a hukumance gwamnati ta haramta wa kafafen yada labarai na cikin gida tattaunawa kan yanayin lafiyarsa.

 

Har ila yau shugaban na Kamaru bai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York ba, da kuma taron kasashe masu magana da harshen Faransanci a birnin Paris.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 22, 2024 October 22, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

NIJERIYA TA ZARGI WANI KAMFANIN KASAR CHINA DA KOKARIN KWACE KADARORIN GWAMNATI.

Attajdid Attajdid August 16, 2024
Jigawa Speaker Calls for Global Action on Girls’ Education, Security, and Safety
100 Days Community Association Commends LG Boss For Purposeful Leadership 
Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 7 a kudancin Gaza
Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?