Wata gobara ta tashi a ma’aikatar iskar gas ta Leviathan da ke gabar tekun Haifa, wanda daya ne daga cikin mafi girman rijiyoyin iskar gas na Palasdinawa da yahudawan sahyoniyya suka kwace.
Gobarar ta tashi ne da daddare, kuma ma’aikatan sun yi iƙirarin cewa ta faru ne saboda “lalacewar wasu na’urorin” Ba da daɗewa ba, gobara ta tashi a wata tashar iskar gas a birnin Ashkelon, kuma sun yi amfani da irin wannan da cewa matsalar wasu na’urorin suka sami matsala a matsayin uzuri, duk da suna cewa na’urorin basayin kuskuren kafin fara yakin, al’amarine mai wahala a yarda da da’awar su.
At-tajdid News




