By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Alhaji  Sunusi Bature Dawakin Tofa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Alhaji  Sunusi Bature Dawakin Tofa
News

An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Alhaji  Sunusi Bature Dawakin Tofa

Attajdid
Last updated: 2024/08/26 at 10:57 AM
Attajdid Published August 26, 2024
Share
SHARE

Kungiyar Daliban karamar hukumar Dawakin Tofa  da asusun tallafawa ilimi na karamar hukumar Dawakin Tofa sun karrama Alhaji  Sunusi Bature Dawakin Tofa bisa namijin kokarin da yake yi na ciyar da dalibai gaba a karamar hukumar.

Sunusi Bature wanda shine mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu shaidar karramawar ne yayin wata ziyarar da kungiyar ta kai masa ofishin sa a ranar Talata.

Karramawar na kunshe cikin wata wasikar godiya da Dr. Mamunu Mustapha ya gabatar a madadin kungiyoyin biyu.Wasikar ta bayyana irin jajircewar da Sunusi Bature ya bayar ga dimbin daliban Dawakin Tofa, musamman daliban dake karatun digiri a Jami’ar Bayero Kano.

Gudunmawar da ya bayar, wandda ta hada da biyan kudaden rajista na zangon karatu na 2023/2024, da shigewa gaba wajen biyawa dalibai matsalolin kudi, Wanda hakan yasu damar mayar da hankali kan karatunsu.

Baya ga tallafin da yake baiwa daliban BUK, Sunusi Bature ya tsallaka  zuwa sauran manyan makarantun gaba da sakandire inda ya aiwatar da makamancin wannan tallafi.

Kazalika Sunusi Bature ya bayar da irin wannan tallafi ga daliban Makarantar fasaha d Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano da ke Gwamai, tare da kara fadada hanyoyin samun ilimi ga matasa a karamar hukumar.

Kungiyoyin sun jaddada cewa tallafin da Sunusi Bature yake bayarwa wajen inganta harkokin ilimi a Dawakin Tofa ya taimaka matuka wajen kara samun dalibai masu ci gaba da karatu.

Sun bukace shi da ya ci gaba da kokarinsa na daukaka matsayin ilimi da samar da damammaki ga matasa a cikin al’umma.A nasa bangaren  Sanusi Bature ya ce ya zama wajibi a kansa ya bada dukkanin gudunmawa domin bunkasa ilimi a karamar hukumar Dawakin Tofa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid August 26, 2024 August 26, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

JIGAWA STATE AT 33: GOVERNOR NAMADI FELICITATES WITH CITIZENS

Attajdid Attajdid August 27, 2024
Dangote Ya Ba Da Tallafin Naira Biliyan 1.5 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Maiduguri
Sakon ‘Yan Gwagwarmayar ‘Yantar Da Kasar   Palastinu Na Duniya 🇵🇸 Da Kasar Labanon
An Gano Gawawwaki da Suka Zagwanye a ƙarƙarshin ɓuraguzan gidaje
Sojojin Isra’ila Suna Fuskantar Barazana Mai Tsanani a Yakin da Suke yi a Gabas ta Tsakiya
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?