Zuwa yanzu ƙasashe 147 ne suka amince da ayyana Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, bayan da Belgium a yau Talata ta kawo ƙarshen doguwar muhawarar da take tafkawa a zauren majalisarta kan wannan ƙudiri tare da amincewa da shirin amincewa da halascin yankin a matsayin cikakkiyar ƙasa.
Yayin zaman babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da zai gudana a watan nan ne Belgium, za ta bayyna amincewa da halascin yankin na Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, kamar yadda Maxine Prevot, mataimakin Firaministan ƙasar ta Turai ke bayyanawa a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X yau Talata.
Prevot ya bayyana cewa baya ga amincewa da halascin ƙasar Falasɗinu, ƙasar za kuma ta lafta takunkumai har guda 12 kan gwamnatin Isra’ila baya ga haramta shigo mata da kayan da aka sarrafa a yankin Yahudawa ƴan kama waje zauna da ke yammacin gaɓar kogin Jordan.
Prevot wanda mamba ne a jam’iyyar masu tsaka-tsakan ra’ayi ta Centrist Le Zangaj ‘Les Engages’, ya ce Belgium ta ɗauki wannan mataki ne la’akari da halin ƙuncin da Isra’ila ta jefa Falasɗinawa musamman a yankin Gaza, sai dai ya ce amincewa da halascin zai fara aiki a hukumance ne bayan Hamas ta saki ilahirin fursunonin da ke hannunta, haka zalika sai ƙungiyar ta janye daga jagorancin Gaza.
Tuni ma’aikatar harkokin wajen Falasɗinu ta yi maraba da matakin tare da kira ga sauran ƙasashe su bi sahu don amincewa da halascin yankin a matsayin ƙasa.
Kawo yanzu ƙasashe 147 ne suka amince za su ayyana yankin na Falasɗinu a matsayin halastacciya, adadi mafi yawa da aka taɓa samu a tarihi tun bayan kafuwar Isra’ila a tsakar yankin da ke ƙarƙashin ikon Birtaniya a lokacin mulkin mallaka.
Wannan adadi na ƙasashe shi ke wakiltar kashi 75 na zaman taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, zaman da ake saran ya mayar da hankali kan halin da ake ciki a Gaza da sauran rikice-rikicen da duniya ke fama da su.
Daga: Muhammad Zangina Kura
At’tajdid News




