By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana
News

Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana

Attajdid
Last updated: 2025/05/25 at 3:17 PM
Attajdid Published May 25, 2025
Share
SHARE

Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana

 

 

Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni huɗu a kammala gasar.

 

 

Salah ya kuma lashe lambar yabo ta ɗan wasan maza na shekara na Ƙungiyar ‘Yan Jarida Marubuta Wasannin Kwallon Ƙafa a karo na uku a farkon wannan watan. / Reuters

24 Mayu 2025

 

 

An sanar da Mohamed Salah a matsayin gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya na bana a ranar Asabar, bayan da ɗan wasan Masar ɗin ya nuna bajinta a kakar wasa ta bana musamman bayan Liverpool ta lashe gasar ta Firimiya a karo na biyu.

 

Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni huɗu a kammala gasar.

 

Bayan samun wannan lambar yabo a kakar 2017-18, Salah ya zama ɗan wasa na biyar a tarihi da ya lashe gasar sau biyu, bayan Thierry Henry, Cristiano Ronaldo, Nemanja Vidic da Kevin De Bruyne.

 

Dan wasan Masar ɗin mai shekara 32 yana kan hanyar lashe wani takalmin zinaren a matsayinsa na wanda ya fi zura ƙwallaye a kakar ta bana inda ya wuce ɗan wasan Newcastle Alexander Isak da ƙwallaye biyar kafin ranar ƙarshe ta kakar wasa a ranar Lahadi.

 

Kafa tarihi

 

Babu ɗan wasan da ya taɓa ci da ba da tallafin jimillar ƙwallaye 46 a salon gasa mai wasanni 38 a kaka guda. A wasan Liverpool da Crystal Palace na gobe Lahadi, idan Salah ya ci ƙwallo ko ya ba da tallafi, zai iya cim ma tarihin ƙwallaye 47 da Alan Shearer da Andrew Cole suka kafa tun a zamanin gasa mai wasanni 42.

 

Sakamakon ya wuce ko wane ɗan wasa wurin bayar da taimakon cin ƙwallaye da taimako shida, akwai yiwuwar Salah ya zama ɗan wasa na farko a tarihi da zai lashe takalmin zinare, da kyautar Golden Playmaker da kuma lambar yabo ta ɗan wasan kaka.

 

Salah ya kuma lashe lambar yabo ta ɗan wasan maza na shekara na Ƙungiyar ‘Yan Jarida Marubuta Wasannin Kwallon Ƙafa a karo na uku a farkon wannan watan.

 

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

AT-TAJDID NEWS

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid May 25, 2025 May 25, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Ana Saran Za a Cimma Mastaya Akan Tsagaita Da Kuma Musayan Bursunonin Falasdinu da Isra’ila.

Attajdid Attajdid September 5, 2024
Wakilan Kasashan Afarka Sunyi Kausasan Bayanai a Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo na 79
GOV. LAWAL PRESENTS N545 BILLION 2025 ‘RESCUE BUDGET 2.0’ TO ZAMFARA ASSEMBLY, PRIORITIZES SECURITY, HEALTH AND EDUCATION
An kashe ‘yan Nijeriya 1,172 da sace fiye da 1,000 a cikin wata tara – NHRC
KANO STATE PILGRIMS WELFARE BOARD ANNOUNCES FINAL HAJJ FARE FOR 2026
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?