Kungiyar Jama’atut Tajdidil Islamy (JTI) yankin Kano ta yamma ta yi amfani da lokacin hutu domin ba da horo ga dalibai domin koyar da su sana’a a yankunan unguwannin Dorayi da Gwale da suke karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano.
An horar da daliban yadda ake hada Solar Panel na tsawon wuni daya a karkashin kulawar kwamatin dake kula da bangaran sana’o’i (Ummal). Daliban da suka samu wannan horarwa sun hada maza da mata ‘yan ajin farko zuwa aji na uku na karamar sakandare (J.S.S 1 – J.S.S 3). An gudanar da shirin horarwa ne a makarantar Firamaren Ja’en Primary dake Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Mai rahoto;
Muhammad Nuru Adam.
At-tajdid News.





