Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta ce ƙasar ta sayar da wutar lantarki ta N58.65bn ga ƙasashen Togo, Benin da Jamhuriyar Nijar a watanni uku na farkon shekarar 2024.
Sannan ta sayar da lantarki na N63.28bn a watanni uku na tsakiyar shekara, kana ta sayar da lantarki na N59.69bn a watanni uku na kusa da ƙarshen shekara ga waɗannan ƙasashe. TRT Afarka Hausa.
Mai rahoto;
M.B.Gama.
At-tajdid News.




