Kungiyar Jama’atut Tajdidil Islamy (JTI) Yankin Kano ta Gabas ta Gabatar da Taron Karawa Juna Sani Akan Tarbiyya da Shaye-shaye Kayan Maye
Taron ya gabatane a karkashin Kwamatin kula da al’amurin tarbiyya na kungiyar, an gunar da shi ne ranar 30 ga Rabi’ul Sani 1445 dai-dai da 2 ga watan Nuwanba 2024, taron ya gabatane a babban dakin taro na hukumar zakka da kubisi ta Jahar Kano da ke kantitin zuwa filin jirgin sama (airport road).
Mataimakin Kwamandan Hisbah Dr. Mujaheedhiddin da Malamai da masana sun gabatar jawabai akan jigon taron tare da janhankali akan illar da shan kayan maye yake haifarwa a cikin al’umma ta bangarori daban-daban.
Mahalarta daga bangarori da dama na Jahar Kano ne suka sami halarta daga cikin akwai Mataimakin Kwamandan Hisbah na Jahar Kano Dr. Mujaheeddin Dr. Aminuddin Abubakar da kuma Jagororin (JTI) na kananan hukumumin Kano ta gabas da kuma na yankuna har yazuwa mazabu tare da ‘yan siyasa.
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




