By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Tarayya, Jihohi da ƙananan Hukumomin Nijeriya Sun Raba Naira Tiriliyan 1.2 a Watan Agusta – FAAC
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin Tarayya, Jihohi da ƙananan Hukumomin Nijeriya Sun Raba Naira Tiriliyan 1.2 a Watan Agusta – FAAC
News

Gwamnatin Tarayya, Jihohi da ƙananan Hukumomin Nijeriya Sun Raba Naira Tiriliyan 1.2 a Watan Agusta – FAAC

Attajdid
Last updated: 2024/09/18 at 12:07 PM
Attajdid Published September 18, 2024
Share
SHARE

Kwamitin gwamnatin tarayya da ke rabon arziƙin ƙasa wato FAAC, ya ce ya raba naira tiriliyan 1.2 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomin Nijeriya waɗanda kuɗi ne da aka samu a matsayin kuɗaɗen shiga a watan Agusta.Kwamitin ne ya sanar da hakan bayan kammala taron da ya gudanar na watan Satumba a Abuja.

Sanarwar da mai magana da yawun ofishin akanta janar na Nijeriya Bawa Mokwa ya fitar a ranar Talata, ta ce kuɗin da aka raba a wannan karon sun ragu da kashi 11 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda aka raba a watan Yuli.

A watan Yulin bana an raba naira tiriliyan 1.358 wanda hakan ke nufin an samu raguwa da naira biliyan 155.

Ofishin akanta janar ɗin ya bayyana cewa kuɗaɗen shigar sun haɗa da waɗanda aka samu daga kamfanoni wanda ya kai naira biliyan 186.636 da na haraji kan kayayyaki wanda ya kai naira biliyan 533.895 da wanda aka samu daga ɓangaren tura kuɗi ta banki wanda ya kai naira biliyan 15.02 da haraji kan bambancin kuɗi da ya kai naira biliyan 468.25.

Bawa ya kara da cewa daga cikin naira tiriliyan 1.203 da aka raba a matsayin kuɗin shiga, gwamnatin tarayya ta samu jimillar kudi naira biliyan 374.93 sannan gwamnatocin jahohin sun samu jimillar kudi naira biliyan 422.86.

Sai kuma kananan hukumomi sun samu jimillar kudi naira biliyan 306.53 kuma an raba jimillar naira biliyan 99.47 (kashi 13 na kudaden shiga na ma’adinai) da jihohin da suka amfana a matsayin kudaden shiga.

TRT Afarka Hausa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid September 18, 2024 September 18, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

More than 900 Hajj pilgrims die in Saudi Arabia over excessive heat

admin admin July 15, 2024
Hamas ta Bayyana Sunayen Isra’ilawa uku da za ta Saki Gobe Asabar
Gwamnatin tarayya ta Sha alwashin ta na yin amfani da nagarta da kwazon matasan Najeriya wurin ciyar da tattalin Arzikin kasar nan gaba.
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Babban Mufti Nazir Ayyad na kasar Masar ya ce tallafawa al’ummar kasar Falasdinu wani muhimmin aiki ne na addini da kuma kasa wanda bai kamata a yi watsi da su ba.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?