By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Sami Ambaliyar a Nigar Da Rayi Tafiyar Ruwa Da Wasu Manyan Tituna a Birnin Yamai.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > An Sami Ambaliyar a Nigar Da Rayi Tafiyar Ruwa Da Wasu Manyan Tituna a Birnin Yamai.
International News

An Sami Ambaliyar a Nigar Da Rayi Tafiyar Ruwa Da Wasu Manyan Tituna a Birnin Yamai.

Attajdid
Last updated: 2024/08/24 at 9:39 AM
Attajdid Published August 24, 2024
Share
SHARE

Manyan hanyoyin shiga da fita daga Yamai babbar birnin Jamhuriyar Nijar sun kusan katsewa baki ɗaya daga sauran sassan ƙasar sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da ya mamaye yankin Sahel tun daga watan Yuni.

Kwalekwale sun maye gurbin motocin da babura a kan hanyoyin sakamakon ambaliyar ruwa da tamamaye  Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Manyan hanyoyin fita da shiga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar mai kimanin mutum miliyan 1.5 sun kusan katsewa baƙi ɗaya, kana sama da mazauna birnin mutum 11,500 ne iftila’in ambaliyar ruwan sama ya shafa.A watanni uku da suka wuce, ambaliyar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 217 a faɗin ƙasar kana ta shafi sama da mutane 350,000, a cewar gwamnatin mulkin soji ta Nijar.

Da farko dai birnin Yamai ya tsira daga sauran yankunan kudu maso yammacin Nijar, amma a yanzu, kwale-kwale ne suka maye gurbin ƙanana da manyan motoci da babura wajen jigilar mutane da kayayyaki a kan hanyoyi.

Don samun damar isa zuwa ga sauran sassan ƙasar, ”dole sai mutum ya yi amfani da kwale-kwale tare da fatan samun abin hawa idan ya isa ɗaya bangaren,” in ji Habibulaye Abdoulaye, wani mazaunin wata unguwa da ke kewaye da ruwa.

Yawancin kamfanonin sufuri a Yamai sun dakatar da zirga-zirga zuwa sauran sassan Nijar.Yayin da yake kallon yadda ambaliyar ruwan ke gudu ta gefen birnin, wani direban mota Ali Adamou ya shaida wa kamfanin dillacin labarai Faransa AFP cewa ruwan ya tafi da motarsa tare da wasu guda hudu.

“Na kusan mutuwa a lokacin da wata ƙaramar motar bas ta nutse,” in ji A damou Gyara hanyoyi Masu tuƙa ƙananan jiragen ruwa suna karɓar CFA 500 kan duk jigilar da suka yi sai kuma ‘yan sanda da kwale-kwalen sojoji waɗanda suke taimakawa wajen jigilar mazauna da suka maƙale.

Daga gabashin babban birnin ƙasar, kamfanin gine-gine na ƙasar Faransa Sogea-Satom na ƙoƙarin sake buɗe hanyar ƙasa ta ɗaya, babbar hanyar da ta kai tsawon kilomita 1,500.

A gaɓar kogin Neja da ke birnin Yamai, masu aikin tono suna can suna aikin samar da hanyoyin wucewar ruwan, yayin da masu aikin sa kai da sojoji suke zagayawa don toshe wurare da ruwan ya yi wa illa da yashi.

A kwanakin baya ne aka sake buɗe hanya ɗaya tilo ta Tera da manyan motoci suke wucewa daga Yamai zuwa arewacin Burkina Faso.

“Hukumomin jihar suna yin dukkan mai yiwuwa don maido da zirga-zirgar ababen hawa,” in ji Ministan Sufuri, Kanar Salissou Mahaman Salissou.

Hukumomin Nijar dai na fargabar tsawaita zirga-zirgar na iya haifar da ƙaranci man fetur.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 24, 2024 August 24, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Declares Free Medical Treatment For Livestock In an effort to enhance food security, boost the rural economy, and improve animal husbandry practices.

Attajdid Attajdid September 28, 2024
An Kai Hari Akan Bututun Mai a Nigeria 
SAKON TA’AZIYAR SARKIN GOBIR NA SABON BIRNI.
Gwamnatin Tarayya zata Kammala Gyara Hanyar Jirgin Kasa Abuja-Kaduna Cikin Kwanakinnan 10
RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?