Gwamnatin ta Kano ta zargi Dr Ganduje da Murtala Sule Garo da Lamin Sani da kuma Muhammad Takai ne, da karkatar da kudin sama da Naira miliyan dubu 57 na kananan hukumomin Kano 44 . Hakan ya sa ta shigar da kara. Wanda ta shaida cewa kudede ne na tallafin ga Al’ummar karkara, aka karkatar da su zuwa wasu kamfanoni da asusun dai-dai kun mutane.
Gwamnatin Kano, ta kuma zargi waɗanda ake tuhuma da canza kuɗaɗen zuwa daloli, don sayan wasu kadarorin da suka haɗa da ; wurin zama na musamman a kan titin Murtala Muhammad a Kano, wani fili na kasuwanci a Dubai, wani Otal mai darajar biliyoyin Naira a Abuja, da gidajen mai da dama a Kano.
Kundin ƙarar ya nuna cewa jihar kano tana shirin kirawo shaidu 143 a cikin shari’ar
Attajdid News.




