By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: YUNWA, RASHIN TSARO – ME KE KAWO SU? MENENE MAGANIN SU? DAGA ALKUR’ANI MAI GIRMA.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > Feature/Articles > YUNWA, RASHIN TSARO – ME KE KAWO SU? MENENE MAGANIN SU? DAGA ALKUR’ANI MAI GIRMA.
Feature/Articles

YUNWA, RASHIN TSARO – ME KE KAWO SU? MENENE MAGANIN SU? DAGA ALKUR’ANI MAI GIRMA.

Attajdid
Last updated: 2024/08/02 at 9:10 PM
Attajdid Published August 2, 2024
Share
SHARE

Yau Juma’ah, 2/8/2024, an shiga cikin wuni na biyu daga cikin wuni goma da aka ce za a yi ana zanga-zangar nuna fushi da gwamnatin tarayyar Najeriya.

Manyan dalilan yin wannan zanga-zangar guda biyu ne: tsadar kayan masarufi da rashin darajar kudi, ko ma rashinsu a hannu, wanda ya jefa mutane cikin halin yunwa da tagayyara; sai kuma rashin tsaro wanda ya sabbabar hasarar rayukka da dukiya, ya kuma hana walwala. Masu zanga-zangar sun ta’allaka wadannan matsaloli da ma wasunsu ga rashin samun kyakkyawan jagoranci.

A cikin Alkur’ani mai girma a cikin Suratun Nahl (surah ta 16), aya ta 112, Allah Madaukakin Sarki Ya yi bayanin abinda ya sa a kan jarabci al’umma da yunwa da rashin tsaro, Ya kuma bayar da mafita.

Allah Ta’ala Ya ce:

(وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا قَرۡيَةٗ كَانَتۡ ءَامِنَةٗ مُّطۡمَئِنَّةٗ يَأۡتِيهَا رِزۡقُهَا رَغَدٗا مِّن كُلِّ مَكَانٖ فَكَفَرَتۡ بِأَنۡعُمِ ٱللَّهِ فَأَذَٰقَهَا ٱللَّهُ لِبَاسَ ٱلۡجُوعِ وَٱلۡخَوۡفِ بِمَا كَانُواْ يَصۡنَعُونَ)

“Kuma Allah Ya buga misali da wata Alkarya (wata kasa) wadda ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali, arzikinta yana zo mata da yawa daga ko ina, amma sai ta kafurce ma ni’imomin Allah, sai kuwa Allah Ya dandana mata tufafin yunwa da tsoro (rashin tsaro) saboda abinda suka zamo suna aikatawa”

A wannan aya zamu fa’idantu da cewar:

1- Da farko wannan Alkarya tana rayuwa bisa tsarin Allah, don haka Ya saukar masu da aminci da kwanciyar hankali , sannan Ya bunkasa tattalin arzikinsu suka wadata.

2- Daga baya sai suka kafurce ma ni’imomin Allah (wadata da zama lafiya), suka saki hanyar Allah suka koma bin son ransu ko son ran wasu. Wannan canji da suka yi ya sa shima Allah Ya canja masu da akasin ni’imomin da Ya yi masu da farko, Ya saukar masu da yunwa da rashin tsaro.

3- Zamu fahimci cewar idan wata kasa ta samu kanta cikin wannan jarrabawa to ya kamata su gane sun saki hanyar Allah ne, sai su koma mata, watau su bi tsarin musulunci a cikin dukkan bangarorin rayuwa, to Allah zai sake dawo masu da wadannan ni’imomi biyu da Ya kwace masu.

Allah Ka bamu ikon gyarawa, Ka kuma yi muna canji kyakkyawa.

Modibbon Gusau.
27/01/1446.
02/08/2024.

You Might Also Like

Who is Yazeed Shehu Umar Danfulani???

SAKON TA’AZIYAR SARKIN GOBIR NA SABON BIRNI.

HUNGER PROTEST: WE NEED URGENT INTERVENTION OF THE NATIONAL PEACE COMMITTEE .

MENENE AIKIN KUNGIYAR (HAMAS)????

INUWAR JAMA’AR AREWA. Saqo na Musamman game da Zanga Zangar Tsadar Rayuwa

Attajdid August 2, 2024 August 2, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
1 Comment
  • Abdullahi Muhammad Sharif says:
    August 3, 2024 at 8:59 am

    Ameen Amen Allah

    Reply

Leave a Reply to Abdullahi Muhammad Sharif Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Harin Isra’ila ya kashe sama da mutum 50 a Gaza cikin ƙasa da mako guda

Attajdid Attajdid May 15, 2025
An Rantsar da Fafaroma 14 Leo
Remi Tinibu Console Jigawa First Lady Over Son death 
SOJOJIN ISRA’ILA SUNA CIGABA DA KAMA FALASDINAWA
IRAN EXECUTED ISRAEL CONVICTED SPY
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?