Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kasafin kudin jihar Kano na 2025 na biliyan dari bakwai da sha tara da miliyan dari bakwai da hamsin da biyar da dubu dari hudu da sha bakwai, da dari shida da sittin da uku (₦719,755,4107,63).
Haka na kunshe ne cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai jiya mai dauke da sa hannun mai magana da yawun majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai. Radio Kano.
Mai rahoto;
M.B.Gama.
At-tajdid News.





