By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Nijeriya ta Sake Tsunduma Cikin  Gagarumin Rashin Wutar Lantarki
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Nijeriya ta Sake Tsunduma Cikin  Gagarumin Rashin Wutar Lantarki
News

Nijeriya ta Sake Tsunduma Cikin  Gagarumin Rashin Wutar Lantarki

Attajdid
Last updated: 2024/10/20 at 10:55 AM
Attajdid Published October 20, 2024
Share
SHARE

Tsarin samar da wutar lantarki a Nijeriya ya kuma samun tasgaro sakamakon ‘gazawar tsarin’ samar da wutar a safiyar Asabar ɗin nan. Wannan ya janyo birane da garuruwa sun kasance cikin duhu.

 

Kamfanonin samar da lantarki da dama sun tabbatarwa kwastomominsu cewa an samu gazawar babban layin samar da lantarki na ƙasar, wanda wannan ne karo na uku a mako guda, cewar jaridun ƙasar.

 

“A halin yanzu muna aiki tare da takwarorinmu don ganin an gaggauta maido da babban layin wuta,” cewar kamfanin samar da lantarki na Eko electricity distribution company da ke kudu masu yammacin ƙasar, a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

 

Hanyoyin wutar lantarki a Nijeriya, wadda ke da tattalin arziƙi mafi girma a Afirka, yana yawan samun matsaloli, kuma hakan yana tilastawa gidaje da kamfanoni amfani da janareta.

 

Sashen samar da wutar lantarki na ƙasar yana fuskantar tarin ƙalubale, ciki har da gazawar babban layin wuta, da ƙarancin gas, da bashin kuɗin wuta, da kuma lalata kayayyakin samar da wuta.

 

Ƙasar tana da ƙarfin iya samar da lantarki na megawatt 12,500, amma tana iya samar da kusan kwatan adadin ne kacal, wanda ya janyo al’ummar ƙasar suke dogaro kan janareta wanda ke da tsadar amfani.

 

A watan Afrilu, gwamnati Nijeriya ta ƙara kuɗn wuta kan manyan kwastomomi da kashi 230 cikin ɗari.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid October 20, 2024 October 20, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

CBN Na Barazanar Rufe Kashi 95% na Kamfanonin Musayar Kuɗi

Attajdid Attajdid May 17, 2025
Dakarun Hadaka na ‘Yan Gwagwarmayar ‘Yantar da Kasar Palestine a Gaza Sun kai Wasu Jerin Hare-hare Ga ‘Yan Kama Wuri Zauna
Koto Tayi Watsi Da Bukatar jam’iyyar APC na Hana Hukumar KANSIEC Zaɓen Kananan Hukomomi a Jahar Kano
TRUMP AND CHRISTIAN GENOCIDE IN NIGERIA
GOVERNOR DAUDA LAWAL @ 59:
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?