{"id":5408,"date":"2025-12-10T16:08:01","date_gmt":"2025-12-10T16:08:01","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5408"},"modified":"2025-12-10T16:08:01","modified_gmt":"2025-12-10T16:08:01","slug":"zanga-zanga-ta-%c9%93arke-kan-zargin-sojoji-da-kashe-mata-a-adamawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5408","title":{"rendered":"Zanga-zanga ta \u0253arke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa"},"content":{"rendered":"<p>Zanga-zanga ta \u0253arke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa.<\/p>\n<p>Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin Mata sun fito zanga-zangar ne sakamakon rikicin da ya \u0253arke tsakanin kabilu Bachama da Chobo.<\/p>\n<p>A lokacin zanga-zangar an ruwaito cewar mata bakwai ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata.<\/p>\n<p>Shaidu sun ce sojoji sun bu\u0257e musu wuta yayin da suke tare hanya, suna zargin rundunar da goyon bayan wata \u0199abila.<\/p>\n<p>Sai dai rundunar Sojin Najeriya ta musanta wannan zargi.<\/p>\n<p>Ta ce dakarun sun yi artabu ne da wasu \u2018yan bindiga a yankin, kuma ta ce mutuwar wasu mata biyu ya faru ne sakamakon bu\u0257e wuta da \u2018yan bindigar suka yi, ba wai sojoji suka harbe su ba.<\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Adamawa, ta ayyana dokar hana fita na awa 24 a Lamurde domin daidaita al\u2019amura da zaman lafiya.<\/p>\n<p>A Numan, matan da suka sanya riga \u0257auke da launin ba\u0199i ne suka fara zanga-zangar a manyan tituna, inda suke neman yi wa wa\u0257anda aka kashe adalci.<\/p>\n<p>An riga an binne wasu daga cikin wa\u0257anda suka rasu, lamarin da ya \u0199ara haifar da damuwa a tsakanin al\u2019ummar yankin.<\/p>\n<p>\u018aan Majalisa mai wakiltar yankin, Kwamoti Laori, ya yi Allah-wadai da kisan, inda ya ce ya kamata a gudanar da bincike mai zurfi.<\/p>\n<p>Ya bu\u0199aci hukumomin tsaro da su \u0257auki matakin da ya dace, tare da tabbatar da zaman lafiya ba tare da tauye ha\u0199\u0199in \u0257an Adam ba.<\/p>\n<p>Mazauna yankin sun ce rigimar ta jefa mutane cikin tsoro, wanda hakan ya sa da dama suka tsare daga gidajensu.<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid News<\/p>\n<p>Shugabannin al\u2019umma a yankin, sun yi kira da a yi sulhu domin kaucewa \u0199arin tashin hankali.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Zanga-zanga ta \u0253arke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa. Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin Mata sun fito zanga-zangar ne sakamakon rikicin da ya \u0253arke tsakanin kabilu Bachama da Chobo. A lokacin zanga-zangar an ruwaito cewar mata bakwai ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata. Shaidu sun ce sojoji sun [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5409,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5408","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5408","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5408"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5408\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5410,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5408\/revisions\/5410"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5409"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5408"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5408"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5408"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}