{"id":5254,"date":"2025-09-22T06:33:56","date_gmt":"2025-09-22T06:33:56","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5254"},"modified":"2025-09-22T06:34:53","modified_gmt":"2025-09-22T06:34:53","slug":"birtaniya-australia-da-canada-sun-amince-da-falas%c9%97inu-a-matsayin-%c6%99asa-gabanin-babban-taron-mdd","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5254","title":{"rendered":"Birtaniya, Australia da Canada sun amince da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa gabanin babban taron MDD"},"content":{"rendered":"<p>\u0198asashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa, inda suka shiga cikin jerin \u0199asashen Yamma da ke goyon bayan samun &#8216;yancin Falas\u0257inu yayin da ya\u0199in Gaza ke ci gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan na zuwa ne a yayin da Isra&#8217;ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza \/ Reuters<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u0198asashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa, inda suka shiga cikin jerin \u0199asashen Yamma da ke goyon bayan samun &#8216;yancin Falas\u0257inu yayin da ya\u0199in Gaza ke ci gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Birtaniya<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cA sakamakon wannan bala&#8217;in da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, muna \u0257aukar mataki don tabbatar da yiwuwar zaman lafiya da mafitar two-state solution {wato \u0199asashe biyu wadda kowace ke cin gashin kanta},\u201d in ji Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a cikin wani bidiyo da ya fitar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce wannan yana nufin samun Isra&#8217;ila mai aminci da tsaro tare da Falasdinu mai \u0257orewa, inda ya \u0199ara da cewa: \u201cA halin yanzu, ba mu da ko \u0257aya.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A watan Yuli, Firaministan ya ce Birtaniya za ta amince da Falas\u0257inu a watan Satumba idan gwamnatin Isra&#8217;ila ba ta \u0257auki matakan da suka dace ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A gefe guda, gwamnatin Isra&#8217;ila ta bayyana matakin Birtaniya a matsayin \u201cabin dariya\u201d kafin sanarwar ta fito.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kafin sanarwar, mataimakin Firaminista David Lammy ya shaida wa BBC cewa \u201cyanzu lokaci ne da ya dace mu tsaya tsayin daka don mafitaf two-state solution.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Canada<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Firaministan Canada Mark Carney, a ranar Lahadi ya sanar da cewa \u0199asarsa ta amince da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa, tare da yin al\u0199awarin ha\u0257in kai don gina zaman lafiya tsakanin Falas\u0257inu da Isra&#8217;ila.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cCanada ta amince da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa kuma za ta bayar da ha\u0257in kai wajen gina makoma mai zaman lafiya ga Falas\u0257inu da Isra&#8217;ila,\u201d in ji Carney a shafin sada zumunta na X kafin taron Majalisar \u018ainkin Duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanarwar ta biyo bayan furucin Canada a baya na niyyar amincewa da Falas\u0257inu a lokacin zaman taron Majalisar \u018ainkin Duniya karo na 80 a watan Satumba 2025.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Australiya<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ita ma Australiya ta bi sahun takwarorinta wato Canada da Birtaniya wurin amincewa da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa wanda wannan wani yunkuri ne na farfa\u0257o da mafita ta two-state solution wanda zai fara da tsagaita wuta a Gaza da sakin wa\u0257anda aka kama a can, in ji Firaminista Anthony Albanese a cikin wata sanarwa ta ha\u0257in gwiwa tare da Ministan Harkokin Waje Penny Wong.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A baya, Faransa, Luxembourg, da Malta sun sanar da shirin su na amincewa da Falas\u0257inu a taron Majalisar \u018ainkin Duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mustapha Garba Usman<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid News<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198asashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falas\u0257inu a matsayin \u0199asa, inda suka shiga cikin jerin \u0199asashen Yamma da ke goyon bayan samun &#8216;yancin Falas\u0257inu yayin da ya\u0199in Gaza ke ci gaba. &nbsp; Wannan na zuwa ne a yayin da Isra&#8217;ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5256,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5254","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5254","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5254"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5254\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5255,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5254\/revisions\/5255"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5256"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5254"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5254"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5254"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}