{"id":5212,"date":"2025-09-13T17:56:49","date_gmt":"2025-09-13T17:56:49","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5212"},"modified":"2025-09-13T17:56:49","modified_gmt":"2025-09-13T17:56:49","slug":"gwamna-jihar-gombe-muhammadu-inuwa-yahaya-ya-umarci-hukumar-bada-agajin-gaggawa-ta-jihar-sema-da-ta-mika-kayan-tallafi-ga-wadanda-ambaliyar-ruwa-ta-shafa-biyo-bayan-ambaliyar-da-ruwa-da-ta-afku-kum","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5212","title":{"rendered":"Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe."},"content":{"rendered":"<p>Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yayin mika kayan tallafin a fadar dagacin yankin a ranar Laraba, Sakataren gudanarwa na SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna, ya ce gwamna Inuwa Yahaya ne ya amince da bayar da kayan tallafin, wadanda suka kunshi kayan abinci da na masarufi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kayan da aka raba sun hada da buhunan shinkafa, taliya, tabarma, zannuwa, da tufafin yara, da sauransu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cikin jawabinsa ga wa\u0257anda al&#8217;amarin ya shafa, dan majalisa mai wakiltar Kaltungo East kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe, Ladan Yerima Gaule, ya tabbatar da cewa gwamnati na da cikakken kudiri wajen kula da walwalar al\u2019ummarta a kowane hali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ladan ya kuma bukaci jama\u2019a da su ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali, tare da nuna biyayya da goyon baya ga gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya domin ci gaba ya wadata ko\u2019ina a fadin jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa bangaren, Sarkin Jalingo-Kamo, Abdullahi Musa, wanda ya karbi kayan a madadin mutanen da ambaliyar ta shafa, ya jinjinawa Gwamna Yahaya, \u2019yan majalisar jihar da hukumar SEMA bisa wannan taimako.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA da ta mika kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan ambaliyar da ruwa da ta afku kuma ta yi sanadiyyar shafar sama da gidaje 90 a yankin Jalingo-Kamo a jihar ta Gombe. &nbsp; Yayin mika kayan tallafin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5213,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5212","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5212","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5212"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5212\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5214,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5212\/revisions\/5214"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5213"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5212"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5212"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5212"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}