{"id":5203,"date":"2025-09-13T15:37:01","date_gmt":"2025-09-13T15:37:01","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5203"},"modified":"2025-09-13T15:37:01","modified_gmt":"2025-09-13T15:37:01","slug":"yan-nigeria-sun-koka-akan-barazanar-da-suke-fuskanta-a-african-ta-kudu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5203","title":{"rendered":"Yan Nigeria sun koka akan barazanar da suke fuskanta a African ta kudu"},"content":{"rendered":"<p>\u2018Yan Nigeria da ke zaune a kasar Afirka ta Kudu sun koka da yadda su ke fama da Barazana da kuma Kyama daga Kungiyar nan da ta yi Kaurin suna wajen Kyamar \u2018Yan cirani wato \u2018Operation Dudula&#8217;.<\/p>\n<p>Shugaban Kungiyar \u2018Yan Nigeria mazauna kasar Afirka ta Kudu Frank Onyekwelu ya bayyana hakan inda ya yi kira da a gaggauta daukar matakan diflomasiyya a sakamakon rahoton hare-hare da cin zarafi da Kungiyar ta a fatattaki \u2018Yan cirani ta ke musu da kuma yadda su ka haramtawa \u2018Yan kasashen ketare amfana da Asibitocin kasar ta Afirka ta Kudu.<\/p>\n<p>A cewar rahotanni koken na \u2018Yan Nigeria na da nasaba da yadda tun a farkon shekarar nan su ka yi fama da kyama daga Kungiyar da kuma yadda a halin yanzu su ke cike da fargabar bullar wani sabon salon kyama da kuma hantara daga Kungiyar ta a Kori \u2018Yan cirani.<\/p>\n<p>A wani fefen Bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta an ga yadda shuwagabannin Kungiyar ta a fatattaki \u2018yan cirani a Afirka ta kudu su ka yi ta ba da umarnin a kori \u2018Yan cirani daga Asibitocin kasar.<\/p>\n<p>Shugaban Kungiyar ta \u2018Yan Nigeria mazauna kasar Afirka ta kudu Frank Onyekwelu ya koka da yadda aka fara samun mata masu juna biyu daga cikin \u2018Yan cirani a Afirka ta kudu da su ka fara haihuwa a dandariyar siminti ba tare da samun kulawar likitoci ba, da kuma yadda Asibitocin kasar su ke sallamar majinyata ba tare da ba su kulawa ba.<\/p>\n<p>A cewar rahotanni \u2018Yan kungiyar ta Dudula da ke rajin a fatattaki \u2018Yan cirani daga kasar ta Afirka ta kudu sun yi ikirarin cewa su na yaki ne da masu shiga kasar ba bisa ka&#8217;ida ba, da masu safarar kwaya da kuma masu mamaye guraben aiyukan yi da ya kamata al&#8217;ummar kasar su amfana da su.<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Nura Abubakar Musa<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u2018Yan Nigeria da ke zaune a kasar Afirka ta Kudu sun koka da yadda su ke fama da Barazana da kuma Kyama daga Kungiyar nan da ta yi Kaurin suna wajen Kyamar \u2018Yan cirani wato \u2018Operation Dudula&#8217;. Shugaban Kungiyar \u2018Yan Nigeria mazauna kasar Afirka ta Kudu Frank Onyekwelu ya bayyana hakan inda ya yi kira [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5204,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5203","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5203","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5203"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5203\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5205,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5203\/revisions\/5205"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5204"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5203"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5203"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5203"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}