{"id":5196,"date":"2025-09-09T19:47:38","date_gmt":"2025-09-09T19:47:38","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5196"},"modified":"2025-09-09T19:47:38","modified_gmt":"2025-09-09T19:47:38","slug":"gamnatin-nigeria-tana-kokarin-kammala-tsarin-manufofin-iyali-na-kasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5196","title":{"rendered":"Gamnatin Nigeria tana kokarin kammala tsarin manufofin iyali na kasa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Nijeriya tana yun\u0199urin kammala tsarin Manufofin Iyali na \u0198asa<br \/>\nGwamnatin Nijeriya na \u0199o\u0199arin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na \u0198asa wato (National Family Policy) don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.<br \/>\nGwamnatin Nijeriya na \u0199o\u0199arin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na \u0198asa wato (National Family Policy) karkarshin jagorancin Ma\u2019aikatar Mata don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.<\/p>\n<p>Da take jawabi a babban taron GS-25 a kan maudu\u2019in \u2018Adalci kan fara ne daga gida: Iyali a matsayin ginshi\u0199in Adalci da Juriya a Al\u2019umma,\u2019 Mataimakiya ta Musamman ga Ministar a kan Harkokin Mata da Ci gaban Jama&#8217;a, Jummai Idonije ta bayyana cewa a yanzu wannan manufar ita ce aka fi bai wa fifiko.<\/p>\n<p>\u201cA karkashin tsarin sabunta fata Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu, GCFR\u2026 Mun karkatar da hankali ma\u2019aikatar zuwa wannan batu, a yanzu haka muna kan shirin kammala manufofin iyali, wannan ya taso ne daga yadda aka kara wa\u2019adin ma\u2019aikatar a yanzu. A da can akwai tsarin amma ba a maganarsa,\u201d in ji ta.<br \/>\nTa kara da cewa an fadada aikin don kula da mutane masu rauni a fadin kasar: &#8220;&#8230; kamata ya yi ta zama ma&#8217;aikatar harkokin mata da ci gaban zamantakewa, don haka a yanzu muna duba batutuwan mata, yara, iyali da kuma marasa galihu. Don yin duk wa\u0257annan, muna sanya daidaitattun hanyoyin aiki da yawa. &#8221;<\/p>\n<p>A kan batun aiwatarwa kuwa cewa ta yi: \u201c\u2026A karkashin Renewed Hope Social Intervention Project 774, aikin zai gudana a kusan duka \u0199ananan hukumomi 774 a karkashin inuwar Ministar Harkokin Mata, wacce duk wannan ke karkashinta.\u201d<\/p>\n<p>Game da cigaban da ake samu a kan cin zarafin jinsi kuwa, ta ce: &#8220;A inda muke, shekaru biyar da suka wuce, ba a nan muke ba a yau. Al&#8217;umma tana canzawa, amma ka da mu bar kowa ya ci zarafin &#8216;yan\u2019uwanmu mata ko &#8216;yan\u2019uwanmu maza. Dole ne a adalci ya fara daga iyali.&#8221;<br \/>\nA nata jawabin, shugabar tsare-tsare da hulda da jama\u2019a a Guinness Nigeria Chioma Momah, ta ce dole ne iyalai su sanya adalci da juriya a zu\u0199atan \u2018ya\u2019yansu tun daga lokacin haihuwa.<\/p>\n<p>&#8220;Gida shi ne makaranta ta farko ta siyasa, mulki da dabi&#8217;u. Yayin da muke jiran manufofin gwamnati, dole ne mu yi koyi da adalci da hada kai a gida.<\/p>\n<p>\u201cIdan muka koya wa yara maza da mata juriya, tausayi da jajircewa; za su aiwatar da su a cikin mu\u2019amalarsu da jama&#8217;a. Duk wanda muka ga yana yin abin da bai dace ba a matsayin babba, to ya zamo asali ne daga gida.&#8221;<\/p>\n<p>A halin da ake ciki, Masanin ilimin halayyar \u0257an\u2019adam, Oluwatoyin Ogunkanmi, ya bukaci iyaye da su dauki kowane yaro a matsayin na musamman, da dinga yin tattaunawa da su da tabbatar da karfi, da sanya su aiki ta hanyar wanda ya fi iyawa ba ta la\u2019akari da jinsi ba, da samar da tsarin horo, da kuma girmama kowa, tana mai cewa yaran da suka tashi ba tare da samun adalci a gida ba za su nuna son kai a cikin al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Mai rahoto<br \/>\nMustapha Garba Usman<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Nijeriya tana yun\u0199urin kammala tsarin Manufofin Iyali na \u0198asa Gwamnatin Nijeriya na \u0199o\u0199arin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na \u0198asa wato (National Family Policy) don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar. Gwamnatin Nijeriya na \u0199o\u0199arin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na \u0198asa wato (National Family [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4703,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5196","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5196","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5196"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5196\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5197,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5196\/revisions\/5197"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4703"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5196"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5196"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5196"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}