{"id":5190,"date":"2025-09-09T19:41:20","date_gmt":"2025-09-09T19:41:20","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5190"},"modified":"2025-09-09T19:41:20","modified_gmt":"2025-09-09T19:41:20","slug":"%c6%99o%c6%99arin-gwamnatin-nijeriya-na-sulhunta-nupeng-da-dangote-ya-ci-tura","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5190","title":{"rendered":"\u0198o\u0199arin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura"},"content":{"rendered":"<p>\u0198o\u0199arin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura<\/p>\n<p>\u0198ungiyar NUPENG ta yi shelar cewa za ta fara yajin aiki daga ranar Litinin, 8 ga watan Satumbar shekarar 2025, kan zargin da ta yi wa kamfanin Dangote cewa yana \u0257aukar matakan da suka sa\u0253a wa dokokin \u0199wadago.<\/p>\n<p>Zaman sirrin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gudanar ranar Litinin da maraice domin sulhuta \u0199ungiyar ma\u2019aikatan dakon man fetur da gas (NUPENG) da kamfanin mai na Dangote ya kasa cim ma nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rahotanni daga Nijeriya sun ce zaman da Ministan \u0198wadagon \u0199asar, Mohammed Dingyadi, da \u0198aramar Ministar \u0198wadago, Nkiruka Onyejeocha, suka jagoranta wani mataki ne na warware ta\u0199addamar da ke tsakanin \u0253angarorin biyu domin kauce wa yajin aikin da \u0199ungiyar NUPENG ta ce za ta yi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wa\u0257anda suka halarci zaman sun ha\u0257a da shugabannin \u0199ungiyar NUPENG da jami\u2019an \u0199ungiyar \u0199wadagon Nijeriya (NLC) da kuma na \u0199ungiyoyin \u0199wadago na TUC.<\/p>\n<p>Kazalika zaman ya samu halartar babban daraktan ajiya da rabawa da sayar da mai na hukumar da ke kula fannin tacewa da sayar da mai ta Nijeriya (NMDPRA), Ogbugo Ukoha, da kuma wakilan kamfanin Dangote da gidan man MRS.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai an kammala taron ba tare da cim ma matsaya ba game da ta\u0199addamar da ake yi tsakanin NUPENG da Matatar Mai ta Dangote.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ranar Juma\u2019ar da ta gabata ne dai \u0199ungiyar \u0199wadagon NUPENG ta yi shelar \u0199addamar da yajin aiki daga ranar 8 ga watan Satumba kan abin da ta kira \u0199o\u0199arin Matatar Man Dangote na hana direbobin tankokin dakon mai na CNG \u0257insa shiga \u0199ungiyoyin \u0199wadago.<\/p>\n<p>Duk da cewa \u0199ungiyoyin \u0199wadagon direbobin tankokin dakon mai na PTD da DTCDA sun nesanta kansu da wannan matakin, NUPENG ta tabbatar ranar Lahadi cewa za ta tsunduma cikin yajin aikin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Domin ta kauce wa wannan yajin aikin, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi kira ga \u0199ungiyar \u0199wadagon ranar Lahadi ta sake tunani kan wannan matakin nata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dingyadi, a wata sanarwar da shugabar sashen sadarwa ta ma\u2019aikatarsa, Patience Onuobia, ta fitar, ya yi kira ga NUPENG ta dakatar da yajin aikinta domin ba da damar tattaunawa.<\/p>\n<p>Ministan na \u0198wadago ya kuma yi kira ga NLC ta janye shawarar da ta bai wa \u0199ungiyoyin da take da ala\u0199a da su na kasancewa cikin shirin shiga yajin aikin goyon bayan NUPENG kan abin da ta kira \u201cmatakan \u0199in jinin ma\u2019aikata da \u0199ungiyoyin \u0199wadago\u201d na kamfanin Dangote.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya ce, \u201cna kira duk masu ruwa da tsaki domin wani zaman sasantawa ranar Litinin 8 ga watan Satumba na shekarar, 2025. Tun da na riga na sa baki, na ro\u0199i NUPENG ta janye matakin da ta \u0257auka na rufe fannin man fetur daga gobe\u201d .<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cFannin man fetur na da humimmi ga wannan \u0199asar. Ya \u0199unshi asalin tattalin arzi\u0199in \u0199asar. Yajin aiki , ko na rana \u0257aya ne, zai yi tasiri mai muni, da zai janyo asarar biliyoyin naira da kuma wahala mai tsanani ga \u2018yan Nijeriya,\u201d in ji ministan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto<\/p>\n<p>Mustapha Garba Usman<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198o\u0199arin gwamnatin Nijeriya na sulhunta NUPENG da Dangote ya ci tura \u0198ungiyar NUPENG ta yi shelar cewa za ta fara yajin aiki daga ranar Litinin, 8 ga watan Satumbar shekarar 2025, kan zargin da ta yi wa kamfanin Dangote cewa yana \u0257aukar matakan da suka sa\u0253a wa dokokin \u0199wadago. Zaman sirrin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5191,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5190","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5190","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5190"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5190\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5192,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5190\/revisions\/5192"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5191"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5190"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5190"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5190"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}