{"id":5055,"date":"2025-08-19T07:46:32","date_gmt":"2025-08-19T07:46:32","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5055"},"modified":"2025-08-19T07:46:32","modified_gmt":"2025-08-19T07:46:32","slug":"ministan-kula-da-albarkatun-teku-adegboyega-oyetola-ya-sha-alwashin-rage-dogaron-nigeria-akan-shigo-da-kifi-daga-kasashen-ketare-ta-hanyar-habaka-noman-kifi-a-cikin-gida-tare-da-kyautata-fasahar-kiwon","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=5055","title":{"rendered":"Ministan Kula da Albarkatun teku Adegboyega Oyetola ya sha Alwashin rage dogaron Nigeria akan shigo da kifi daga kasashen ketare ta hanyar habaka noman kifi a cikin gida tare da kyautata fasahar kiwon kifi a fadin Nigeria."},"content":{"rendered":"<p>Ministan Kula da Albarkatun teku Adegboyega Oyetola ya sha Alwashin rage dogaron Nigeria akan shigo da kifi daga kasashen ketare ta hanyar habaka noman kifi a cikin gida tare da kyautata fasahar kiwon kifi a fadin Nigeria.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakanan ministan ya bayyana tsare-tsaren karfafa guiwar matasa da kuma mata da kayan aiki da ake bukata ta yadda za su yi fice a habakar tattalin arziki daga teku.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya kara da cewa Nigeria ta na kan turbar cin gajiyar dimbin damammakin tattalin arziki da ke a Teku da kogunan ruwa da rafi da kuma kududdufai tun bayan da majalisar zartaswa ta kasa ta amince da dokar kyautata tattalin arzikin kogunan ruwa ta kasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Kamfanin gas na LNG Nigeria Philip Mishelbila ya shedawa shugaban kamfanin mai na kasa Bayo Ojulari bukatar gaggauta zuba jari a fannin makamashin gas domin habaka wadata kasar nan da gas.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Philip ya bayyana hakanne ayayin wata ziyara da shugaban kamfanin mai na kasa Ojulari ya kai masa a kamfaninsa na sarrafa gas da ke a Bonny Island inda ya bayyana gamsuwa da habakar kamfanin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakanan ya bayyana Kamfanin mai na kasa a matsayin abin dogaro ta fuskar zuba jari a saboda yadda ya himmatu wajen samar da gas tare magance kalubalen da ke tattare da rarraba shi a sassan kasar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mujallar Financial Times da ke kula da hadahadar kudade ta duniya ta ce babban taron Afirka da za a yi zai yi duba akan yadda\u00a0 Nigeria da sauran kasashen Afirka su ka rungumi Sabbin sauye-sauye ta fuskar Fasaha da kuma Sauya fasalin tattalin Arziki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron wanda za a gudanar da shi a ranakunn21 da 22 ga watan Oktoban shekarar 2025 a birnin london zai kunshi taken cewa \u2018Afirka a Duniyar da ke fuskantar sauyi\u2019.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce taron zai yi duba akan kwarin guiwar da Afirka ta ke da shi wajen rungumar fasahar Amfani da makamashi da ya ba ya gurbata muhalli da habakar masana&#8217;antu da tasirin matasa a kasuwanci ta fuskar samar da cigaba mai dorewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakanan taron zai yi duba akan yadda aka samar da sauye-sauye a Nigeria da Angola da kuma Afirka ta kudu da kuma cigaban kasashen ta fuskar fasahar zamani ta AI da sauran sauye-sauyen fasahohin zamani<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Kula da Albarkatun teku Adegboyega Oyetola ya sha Alwashin rage dogaron Nigeria akan shigo da kifi daga kasashen ketare ta hanyar habaka noman kifi a cikin gida tare da kyautata fasahar kiwon kifi a fadin Nigeria. &nbsp; Hakanan ministan ya bayyana tsare-tsaren karfafa guiwar matasa da kuma mata da kayan aiki da ake bukata [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":5056,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-5055","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5055","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5055"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5055\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5057,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5055\/revisions\/5057"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5056"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5055"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5055"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5055"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}