{"id":4957,"date":"2025-08-04T10:43:34","date_gmt":"2025-08-04T10:43:34","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4957"},"modified":"2025-08-04T10:43:34","modified_gmt":"2025-08-04T10:43:34","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-ware-naira-biliyan-n712-domin-mayar-da-filin-jirgin-sama-na-mmia-na-legas-sahun-gaba-a-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4957","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin tarayya tace Za ta mayar da filin jirgin sama na Legas cibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Yammacin Afirka bayan shekaru biyu da gyara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gyaran filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas da zai ci kimanin naira biliyan 712.3 zai mayar da filin jirgin zuwa sahun gaba a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan kammala aikin cikin shekaru biyu, ana sa ran filin jirgin zai zama cibiyar zirga-zirgar jiragen sama a Yammacin Afirka.<\/p>\n<p>Ana sa ran za a dauki nauyin aikin gaba daya daga shirin Nan na sabunta Fata da aiyukan more rayuwa, Wanda shugaban kasa ya fito dashi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, da Daraktar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Hajiya Olubunmi Kuku, sun yi karin bayani game da aikin a karshen mako, wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da shi makon jiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan gyara zai hada da canza fasalin ginin Terminal 1 gaba daya, wanda aka kaddamar tun shekarar 1979, da kuma sake tsara Terminal 2 wanda aka fara amfani da shi a karshen mulkin shugaba Buhari.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haka kuma, za a yi wa wuraren ajiye jiragen sama, wuraren ajiye motoci, hanyoyin shiga da fita da kuma sashe na kasa da kasa na filin jirgin sabbin gyare-gyare.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>filin jirgi, wanda shi ne mafi yawan zirga-zirga a Najeriya, na dauke da kashi 67% na dukkan fasinjojin da ke tashi daga cikin kasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hajiya Kuku ta bayyana aikin a matsayin wani babban shiri da zai mayar da MMIA zuwa matakin da zai kai daidaito da ingantattun filayen jirgin sama na duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta ce aikin yana da hangen nesa, domin zai shafi kusan dukkanin muhimman bangarori na filin jirgin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Keyamo ya bukaci wadanda ke sukar aikin da su nemi karin ilimi game da yadda ake kashe kudade wajen gina manyan filayen jiragen sama a duniya kafin su yi sharhi mara tushe.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haka zalika, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Tope Ajayi, da ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana cewa irin wannan sabuntawa na filayen jirgin sama na kasa da kasa yana faruwa a sassan duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hajiya Kuku ta bayyana wasu daga cikin ribar aikin da suka hada da Gyaran sashen wajen ginin, da cikin ginin, ciki har da tsarin bututun ruwa, lantarki domin su daidaita da ka\u2019idodin duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haka kuma, gwamnati za ta gina sabuwar hanyar mota da za ta kasance ta zamani da sauki, domin saukaka cunkoso da bunkasa jin dadin masu zuwa filin jirgin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wani bangare mai muhimmanci na shirin shi ne gyaran fili gaban ginin, domin kara maraba da saukar baki cikin kwarewa da nuna al\u2019adun kasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta ce za a tsara central square da ke gaban filin jirgin yadda zai kasance abin alfahari ga kasa kuma ya zama kyakkyawan hoto na farko ga masu zuwa Najeriya.<\/p>\n<p>Shugabar FAAN ta bukaci hadin kai da fahimtar dukkan masu ruwa da tsaki da fasinjoji yayin da aikin ke gudana.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Nura Abubakar Musa<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya. &nbsp; Gwamnatin tarayya tace Za ta mayar da filin jirgin sama na Legas cibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Yammacin Afirka bayan shekaru biyu da gyara. &nbsp; Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gyaran filin jirgin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4958,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4957","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4957","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4957"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4957\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4959,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4957\/revisions\/4959"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4958"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4957"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4957"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4957"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}