{"id":4949,"date":"2025-08-02T17:13:10","date_gmt":"2025-08-02T17:13:10","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4949"},"modified":"2025-08-02T17:13:10","modified_gmt":"2025-08-02T17:13:10","slug":"ba-zamu-ta%c9%93a-ajiye-makami-ba-har-sai-an-samar-da-%c6%99asar-falas%c9%97inu-hamas","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4949","title":{"rendered":"Ba zamu ta\u0253a ajiye makami ba, har sai an samar da \u0199asar Falas\u0257inu-HAMAS"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u0198ungiyar Hamas ta sake jadadda matakin ta na cewa ba zata ta\u0253a ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da yantacciyar \u0199asar Fala\u0257inu a yankin gabas ta tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake \u0199o\u0199arin \u0199ullawa baya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A halin da ake ciki yanzu haka ana wata tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba tsakanin Isra\u2019ila da Hamas don \u0199ulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60, da kuma sakin mutanen da ke ri\u0199e a hannun \u0253angarorin biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A Talatar da ta gabata ne \u0199asahen Qatar da Masar suka sanar da matakin \u0199asashen Saudi Arabiya da Faransa na goyon bayan samar da \u0199asar Falasdinu, don tabbatar da dawamammen zaman lafiya a gabas ta tsakiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>To amma \u0199asashen sun ce hakan zata yiwu ne kawai idan har Hamas ta amince da ajiye makamai ga mahukuntan Faladinu da ke Ramallah.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wata sanarwa da Hamas \u0257in ta fitar ta ce bazata ta\u0253a ajiye makamai ba, har sai ta tabbatar da samun \u01b4ancin kan Falas\u0257inawa, da kuma ayyana birnin \u0198udus a matsayin babban birni.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan ba shine karon farko da Hamas ke bayyana hakan a matsayin hanya \u0257aya tilo ta ajiye makami ba, yayinda ita kuma Isra\u2019ila ke cewa zata yi kowacce irin tattaunawa da Hamas ne bayan sun amince da ajiye makami.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A makon da ya gabata Prime ministan Isra\u2019ila Benjamin Natenyahu ya ce ba shakka samar da \u01b4antacciyar \u0199asar Falas\u0257inu, shimfida hanya ne na rusa Isra\u2019ila don haka ba zai ta\u0253a aminta da hakan ba, kuma dole ne sha\u2019anin tsaron yankunan Falas\u0257inu ya kasance \u0199ar\u0199ashin ikon \u0199asar sa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake chachakar matakin \u0199asashen Burtaniya, Canada da kuma Faransa na goyon bayan samar da \u0199asar Falas\u0257inu biyo bayan halin da Isra\u2019ila ta jefa al\u2019ummar Gaza, ya ce wannan abu ne da Hamas ta janyo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mujahid Muhammad Tasiu<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid News<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; \u0198ungiyar Hamas ta sake jadadda matakin ta na cewa ba zata ta\u0253a ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da yantacciyar \u0199asar Fala\u0257inu a yankin gabas ta tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake \u0199o\u0199arin \u0199ullawa baya. &nbsp; &nbsp; A halin da ake [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4887,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4949","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4949","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4949"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4949\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4950,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4949\/revisions\/4950"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4887"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4949"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4949"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4949"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}