{"id":4804,"date":"2025-06-20T16:57:10","date_gmt":"2025-06-20T16:57:10","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4804"},"modified":"2025-06-20T16:57:10","modified_gmt":"2025-06-20T16:57:10","slug":"yin-sulhu-da-yan-bindiga-dabara-ce-ba-gazawa-ba-gwamnatin-sakkwato","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4804","title":{"rendered":"Yin sulhu da \u2019yan bindiga dabara ce ba gazawa ba \u2014 Gwamnatin Sakkwato"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin ta ce ba rauni ne ya sa za ta yi sulhu da &#8216;yan bindiga ba.<\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ba gazawa ba ce ta sa ta yanke shawarar tattaunawa da \u2019yan bindigar da suka yanke hukuncin ajiye makamansu ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta ce wannan hanya ce mafi kyau da za ta kawo zaman lafiya mai \u0257orewa a jihar.<\/p>\n<p>Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Basharu Altine Guyawa, ya soki wannan mataki na gwamnatin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Amma Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Shawara kan Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya ce manufar gwamnati ita ce ta kawo zaman lafiya, ba don ta kasa ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce, \u201cMun san kowa na da \u2018yancin fa\u0257in albarkacin bakinsa. Amma dole ne mu fayyace dalilin da ya sa Gwamna Ahmed Aliyu ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar rashin tsaro, ciki har da tattaunawa da \u2018yan bindigar da suka tuba.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa abin mamaki ne yadda Guyawa ke sukar wannan yun\u0199uri.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce shi ma ya ta\u0253a bu\u0199atar shirin shiga tsakanin gwamnati da \u2018yan bindiga domin yin sulhu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kanal Usman ya bayyana cewa gwamnati tana amfani da dukkanin matakai biyu; na \u0199arfi da na sulhu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, mutane da yawa a Rabah, Goronyo, Isa, Sabon Birni da wasu yankuna na ta yin hijira.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Manoma sun bar gonakinsu, amfanin gona ya ragu, kuma kasuwanci ya tsaya cak.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan ya jawo \u0199arancin abinci da tsadar rayuwa a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cBurinmu shi ne mu dawo da zaman lafiya, mu dawo da mutane gidajensu, sannan a sake farfa\u0257o da harkokin noma da kasuwanci,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce har yanzu gwamnati na aike jami\u2019an tsaro inda ya dace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Amma wa\u0257anda suka tuba da gaske za a kar\u0253e su bisa kulawa da tsari na gyaran hali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cWannan ba gajiyawa ba ce ko jin tsoro, wannan dabara ce ta sulhu domin \u0257orewar zaman lafiya.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Amma ya ro\u0199i masu sukar gwamnati da su yi magana cikin hankali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cJihar Sakkwato na bu\u0199atar ha\u0257in kai da mafita, ba rabuwar kai da zargi ba. Gwamna Ahmed Aliyu na aiki tu\u0199uru don kawo zaman lafiya.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mustapha Garba Usman<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Attajdid news<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin ta ce ba rauni ne ya sa za ta yi sulhu da &#8216;yan bindiga ba. Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ba gazawa ba ce ta sa ta yanke shawarar tattaunawa da \u2019yan bindigar da suka yanke hukuncin ajiye makamansu ba. &nbsp; Ta ce wannan hanya ce mafi kyau da za ta kawo zaman lafiya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4805,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4804","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4804","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4804"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4804\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4806,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4804\/revisions\/4806"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4805"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4804"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4804"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4804"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}