{"id":4791,"date":"2025-06-17T10:57:23","date_gmt":"2025-06-17T10:57:23","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4791"},"modified":"2025-06-17T10:57:23","modified_gmt":"2025-06-17T10:57:23","slug":"matatar-man-israila-ta-daina-aiki-bayan-sabon-harin-iran","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4791","title":{"rendered":"Matatar man Isra\u2019ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran."},"content":{"rendered":"<p>Matatar man Isra\u2019ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran.<\/p>\n<p>Tue, 17 Jun 2025 10:17:39 GMT+0100<\/p>\n<p>Matatar man \u0199asar Isra&#8217;ila dake yankin Haifa ta dakatar da ayyukanta gaba daya bayan hari da Iran ta kai mata.<\/p>\n<p>Hukumar gudanarwar matatar man \u0199asar Isra\u2019ila dake yankin Haifa ta sanar da cewa matatar ta dakatar da ayyukanta \u0257ungurungum bayan harin da Iran ta kai mata.<\/p>\n<p>Kamfanin Bazan Group dake kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba \u0257aya \u2014 a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke \u0257aukar zafi tsakanin \u0199asashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji.<\/p>\n<p>Bazan Group ya bayyana cewa, harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi.<\/p>\n<p>Harin na Iran ya kuma halaka ma\u2019aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra\u2019ila suka sanar.<\/p>\n<p>Wannan na faruwa a ci gaban hare-haren ramuwar gayya da makamai masu linzami da Iran ke kaiwa, bayan jiragen Isra\u2019ila sun \u0199addamar da hare-hare da kawo yanzu suka yi ajalin mutane sama da 220 a sassan Iran, har da Tehran, Babban birnin \u0199asar.<\/p>\n<p>Kashi 70 na mutanen da Isra\u2019ila ta kashe a Iran mata da \u0199ananan yara ne; da wasu manyan jami\u2019an tsaro da wani masanin kimiyyar makamashin nukiliya.<\/p>\n<p>Majiyar mu ta ruwaito Isra\u2019ila na cewa ta \u0199addamar da hare-haren ne domin da\u0199ile Iran, wadda ke dab da mallakar makamin nukiliya a cikin wannan shekara, ko cikin watanni ka\u0257an masu zuwa.<\/p>\n<p>Ana iya tuna cewa Firaiminista Banjamin Netanyahu ya bayyana cewa hallaka shugaban addinin Iran, Ayatullah Khamene\u2019i zai yi tasiri wajen kawo karshen rikicin.<\/p>\n<p>A nata bangaren Iran ta bayyana cewa Isra\u2019ila za ta yabawa aya za\u0199inta, kan wa\u0257annan hare-haren ragoncin da ta kai wa fararen hula da cibiyoyin soji da tashoshin makamashin nukiliyarta.<\/p>\n<p>Ta kuma bayyana harin bai tsayar da shirinta na nukiliya domin samar da wutar lantarki da sauran abubuwa na zaman lafiya ba.<\/p>\n<p>Ramuwar gayyar Iran ta shafi cibiyoyin sojin Isra\u2019ila da tashar wutar lantarki da matatar mai, baya ga halaka mutane sama da 24 da lalata gine-gine a wurare daban-daban, ciki har da birnin Kudus, da kuma Tel Aviv, babban birnin \u0199asar Isra\u2019ila.<\/p>\n<p>Mai rahoto<br \/>\nMustapha Garba Usman<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid News<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Matatar man Isra\u2019ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran. Tue, 17 Jun 2025 10:17:39 GMT+0100 Matatar man \u0199asar Isra&#8217;ila dake yankin Haifa ta dakatar da ayyukanta gaba daya bayan hari da Iran ta kai mata. Hukumar gudanarwar matatar man \u0199asar Isra\u2019ila dake yankin Haifa ta sanar da cewa matatar ta dakatar da ayyukanta \u0257ungurungum [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4792,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4791","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4791","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4791"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4791\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4793,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4791\/revisions\/4793"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4792"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4791"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4791"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4791"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}