{"id":4778,"date":"2025-06-16T15:58:13","date_gmt":"2025-06-16T15:58:13","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4778"},"modified":"2025-06-16T15:58:13","modified_gmt":"2025-06-16T15:58:13","slug":"trump-ya-hana-shirin-israila-na-kashe-jagoran-addinin-iran-in-ji-jamiin-amurka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4778","title":{"rendered":"Trump ya hana shirin Isra\u2019ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami\u2019in Amurka"},"content":{"rendered":"<p>Netanyahu dai bai tabbatar ko kuma \u0199aryata rahotannin da ke cewa Shugaban Amurka ya hana shirin kashe Ayatollah ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da wani shiri na Isra\u2019ila na kashe jagoran addinin \u0199asar Iran Ayatollah Ali Khamenei, in ji jami\u2019an Amurka. \/ Reuters<\/p>\n<p>2 awanni baya<\/p>\n<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya hana wani shirin Isra\u2019ila na kashe jagoran addinin \u0199asar Iran Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda wani babban jami\u2019in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Mun gano cewa \u2018yan Isra\u2019ila suna da shirye-shiryen kai wa jagoran addinin Iran hari. Shugaba Trump bai amince da haka ba kuma mun shaida wa Isra\u2019ila cewa ka da su aiwatar da matakin,&#8221; in ji jami\u2019in na Amurka ranar Lahadi, inda ya yi magana da neman a \u0253oye sunansa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun da farko, Firaminista Benjamin Netanyahu ya kauce wa wata tambaya game da rahotannin da ke cewa Trump ya umarci \u0199asarsa ka da ta kashe Khamenei.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Ba zan ce komai a kan wannan batun ba,&#8221; kamar yadda ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Amma zan iya shaida maka cewa&#8230; za mu yi abin da muke bu\u0199atar yi, kuma ina tunanin Amurka ta san abin da zai fi dacewa da Amurka,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kalaman na zuwa ne yayin da Isra\u2019ila da Iran suka yi musayar rokoki ranar Lahadi, inda aka shawarci mutanen gari su nemi mafaka yayin da ake jin \u0199arar ababe a saman birnin \u0198udus, kuma rahotanni ke cewa makamai masu linzami na tsaro sun fara aiki a Tehran.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan gomman shekaru na \u0199iyayya da kuma ya\u0199in bayan-fage da suke yi, rikicin na baya bayan nan shi ne na farko da \u0199asashen suka yi musayar wuta mai irin wannan tsananin, lamarin da ya sanya fargaba ta barazanar samun wani rikici da zai iya mamaye dukkan Gabas ta Tsakiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An fara shi ne ranar Juma\u2019a, a lokacin da Isra\u2019ila ta \u0199addamar da wasu jerin hare-hare da suka kashe manyan kwamandojin da kuma masana kimiyyar nukiliya tare da far ma sansanin sojoji da tashoshin nukiliya da kuma gidaje a fa\u0257in \u0199asar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Harin da Tel Aviv ta \u0199addamar ba gaira ba dalili ne ya janyo rikicin, lamarin da ya sa Iran ta \u0199addamar da ramuwar gayya kan Isra\u2019ila.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hare-haren da kuma hare-haren ramuwar gayyar suna ci gaba da wakana tun wancan lokacin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Netanyahu ya kuma bayyana wa kafar Fox News cewa Isra\u2019ila ta kashe babban jami\u2019in le\u0199en asirin Iran Mohammad Kazemi, yana mai cewa nan ba da\u0257ewa ba ne ta &#8220;kashe babban jami\u2019in le\u0199en asirin Iran da mataimakinsa a Tehran&#8221; yayin da jiragen ya\u0199inta suka kai hare-hare babban birnin \u0199asar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Trump ya jaddada cewa Washington, babbar \u0199awar Isra\u2019ila, &#8220;ba ta da hannu &#8221; cikin hare-haren Isra\u2019ila.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Amurka ya jaddada wa kafar ABC News ranar Lahadi cewa Amurka \u201ca halin yanzu\u201d ba ta da hannu a matakan soji.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa shi zai \u201cyarda\u201d idan takwaransa na Rasha Vladimir Putin zai kasance mai shiga tsakani domin warware rikicin.<\/p>\n<p>Rahoto M.B Gama<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid News<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Netanyahu dai bai tabbatar ko kuma \u0199aryata rahotannin da ke cewa Shugaban Amurka ya hana shirin kashe Ayatollah ba. &nbsp; Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da wani shiri na Isra\u2019ila na kashe jagoran addinin \u0199asar Iran Ayatollah Ali Khamenei, in ji jami\u2019an Amurka. \/ Reuters 2 awanni baya Shugaban Amurka Donald Trump ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4779,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4778","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4778","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4778"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4778\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4780,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4778\/revisions\/4780"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4779"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4778"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4778"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4778"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}