{"id":4661,"date":"2025-05-25T15:17:37","date_gmt":"2025-05-25T15:17:37","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4661"},"modified":"2025-05-25T15:17:37","modified_gmt":"2025-05-25T15:17:37","slug":"mohamed-salah-ya-zama-gwarzon-%c9%97an-wasan-gasar-firimiya-a-kakar-bana","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4661","title":{"rendered":"Mohamed Salah ya zama gwarzon \u0257an wasan Gasar Firimiya a kakar bana"},"content":{"rendered":"<p>Mohamed Salah ya zama gwarzon \u0257an wasan Gasar Firimiya a kakar bana<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda \u0199ungiyar \u0199ar\u0199ashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni hu\u0257u a kammala gasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Salah ya kuma lashe lambar yabo ta \u0257an wasan maza na shekara na \u0198ungiyar \u2018Yan Jarida Marubuta Wasannin Kwallon \u0198afa a karo na uku a farkon wannan watan. \/ Reuters<\/p>\n<p>24 Mayu 2025<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An sanar da Mohamed Salah a matsayin gwarzon \u0257an wasan Gasar Firimiya na bana a ranar Asabar, bayan da \u0257an wasan Masar \u0257in ya nuna bajinta a kakar wasa ta bana musamman bayan Liverpool ta lashe gasar ta Firimiya a karo na biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda \u0199ungiyar \u0199ar\u0199ashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni hu\u0257u a kammala gasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan samun wannan lambar yabo a kakar 2017-18, Salah ya zama \u0257an wasa na biyar a tarihi da ya lashe gasar sau biyu, bayan Thierry Henry, Cristiano Ronaldo, Nemanja Vidic da Kevin De Bruyne.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dan wasan Masar \u0257in mai shekara 32 yana kan hanyar lashe wani takalmin zinaren a matsayinsa na wanda ya fi zura \u0199wallaye a kakar ta bana inda ya wuce \u0257an wasan Newcastle Alexander Isak da \u0199wallaye biyar kafin ranar \u0199arshe ta kakar wasa a ranar Lahadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kafa tarihi<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babu \u0257an wasan da ya ta\u0253a ci da ba da tallafin jimillar \u0199wallaye 46 a salon gasa mai wasanni 38 a kaka guda. A wasan Liverpool da Crystal Palace na gobe Lahadi, idan Salah ya ci \u0199wallo ko ya ba da tallafi, zai iya cim ma tarihin \u0199wallaye 47 da Alan Shearer da Andrew Cole suka kafa tun a zamanin gasa mai wasanni 42.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sakamakon ya wuce ko wane \u0257an wasa wurin bayar da taimakon cin \u0199wallaye da taimako shida, akwai yiwuwar Salah ya zama \u0257an wasa na farko a tarihi da zai lashe takalmin zinare, da kyautar Golden Playmaker da kuma lambar yabo ta \u0257an wasan kaka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Salah ya kuma lashe lambar yabo ta \u0257an wasan maza na shekara na \u0198ungiyar \u2018Yan Jarida Marubuta Wasannin Kwallon \u0198afa a karo na uku a farkon wannan watan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mujahid Muhammad Tasiu<\/p>\n<p>AT-TAJDID NEWS<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mohamed Salah ya zama gwarzon \u0257an wasan Gasar Firimiya a kakar bana &nbsp; &nbsp; Salah ya zura kwallaye 28 tare da bayar da taimako 18 don jagorantar kungiyar ta Anfield taka matakin nasara, inda \u0199ungiyar \u0199ar\u0199ashin jagorancin Arne Slot ta zama zakara a gasar duk da saura wasanni hu\u0257u a kammala gasar. &nbsp; &nbsp; Salah [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4662,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4661","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4661","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4661"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4661\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4663,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4661\/revisions\/4663"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4662"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4661"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4661"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4661"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}