{"id":4558,"date":"2025-05-18T10:09:21","date_gmt":"2025-05-18T10:09:21","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4558"},"modified":"2025-05-18T10:09:21","modified_gmt":"2025-05-18T10:09:21","slug":"ban-sauya-she%c6%99a-ba-makircin-siyasa-da-%c6%99arya-ake-min-kwankwaso","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4558","title":{"rendered":"Ban sauya she\u0199a ba, makircin siyasa da \u0199arya ake min \u2014 Kwankwaso\u00a0"},"content":{"rendered":"<p>Ban sauya she\u0199a ba, makircin siyasa da \u0199arya ake min \u2014 Kwankwaso<\/p>\n<p>Jagoran ya ce a yanzu ya za\u0253i yin shiru game da abubuwan da ke faruwa a siyasar \u0199asar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Jagoran jam\u2019iyyar NNPP, Rabi\u2019u Musa Kwankwaso, ya \u0199aryata wani rahoto da ke yawo cewa yana shirin shiga sabuwar ha\u0257akar siyasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wani gajeren sa\u0199o da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana rahoton a matsayin \u201ckarya, ba shi da tushe kuma makircin wasu \u2018yan siyasa ne.\u201d<\/p>\n<p>Ya garga\u0257i jama\u2019a da ka da su yarda da irin wa\u0257annan labarai marasa tushe.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cAn jawo hankalina kan wani rahoto wanda ke bayyana matsayina a ha\u0257in gwiwar siyasa a Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cIna so na fayyace cewa irin wa\u0257annan rahotannin \u0199arya ne, ba su da tushe kuma makircin siyasa ne kawai,\u201d in ji Kwankwaso.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tsohon ministan tsaron, ya bayyana cewa ya za\u0253i ka da ya ri\u0199a yin magana a fili kan wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar \u0199asar nan, amma zai yi magana a lokacin da ya dace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cNa da\u0257e da daina yin sharhi kan abubuwan da ke faruwa a siyasa, kuma zan ci gaba da kaucewa yin haka a halin yanzu,\u201d ya \u0199ara da cewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwankwaso ya bu\u0199aci \u2019yan Najeriya da su dinga dogaro da hanyoyin sadarwarsa a hukumance idan suna son sanin matsayinsa ko ra\u2019ayinsa game da wani abu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cDangane da hakan, ina ro\u0199on jama\u2019a da su ri\u0199a duba ko sauraron sa\u0199onni da ke fitowa daga shafukana da sauran hanyoyin sadarwarta kawai,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aminiya ta ruwaito cewa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban \u0199asa a jam\u2019iyyar NNPP a za\u0253en 2023, har yanzu yana \u0257aya daga cikin manyan \u2019yan siyasar da ake sa ido a kansu kan yiwuwar yin ha\u0257aka da wata tafiya ta siyasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto<\/p>\n<p>Mustapha Garba Usman<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ban sauya she\u0199a ba, makircin siyasa da \u0199arya ake min \u2014 Kwankwaso Jagoran ya ce a yanzu ya za\u0253i yin shiru game da abubuwan da ke faruwa a siyasar \u0199asar nan. &nbsp; Jagoran jam\u2019iyyar NNPP, Rabi\u2019u Musa Kwankwaso, ya \u0199aryata wani rahoto da ke yawo cewa yana shirin shiga sabuwar ha\u0257akar siyasa. &nbsp; A wani [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4559,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4558","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4558","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4558"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4558\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4560,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4558\/revisions\/4560"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4559"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4558"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4558"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4558"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}