{"id":4533,"date":"2025-05-17T04:46:10","date_gmt":"2025-05-17T04:46:10","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4533"},"modified":"2025-05-17T04:46:10","modified_gmt":"2025-05-17T04:46:10","slug":"tajdidin-shehu-dan-fodiyo-tabbatar-da-addini-neman-mulki-ko-kabilanci-5-sheikh-aminu-aliyu-gusau","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4533","title":{"rendered":"TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO &#8211; TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (5). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU"},"content":{"rendered":"<p>TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO &#8211; TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (5).<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A . GABA TA FARKO: AMSAR TAMBAYA TA FARKO TA MANHAJAR TATTAUNAWA (2):<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>TASIRI DA AMFANIN TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO A KASAR HAUSA DA AREWACIN NAJERIYA A ADDINANCE DA SIYASANCE DA ABUNDA YA SHAFI YANAYIN ZAMANTAKEWA DA TATTALIN ARZIKI.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>1 . A ADDINANCE (2).<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>b . YADUWAR ADDININ MUSULUNCI.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Duk Musulmi na kwarai mai kishin addininsa na musulunci, ba wanda wasu fikirori daban suka ratsa shi ba, irin tunanin kabilanci ko kuma izgili da addini ko kishin al&#8217;adun gargajiya, yana murnar yadda Addinin Musulunci ya samu karbuwa da yaduwa da bunkasa da daukaka a kasar Hausa da kasashen da ke makwabtaka da ita, sakamakon Tajdidin Shehu da daular Musulunci da ya samar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tarihi ya tabbatar da cewar duk da ya ke kusan dukkan Sarakunan kasar Hausa sun karbi musulunci da dadewa kafin a haifi Shehu, amma talakawa da yawan gaske suna kan addinansu na maguzanci, na bori da tsafi da bautar iskoki da magiron gida ko da Shehu ya fara wa&#8217;azi. Za mu kara fahimtar hakan idan muka yi la&#8217;akari da cewar har Bature ya karbi mulkin kasar nan bayan shekaru dari na daular Shehu akwai maguzawa da yawa a cikin dukkan masarautun kasar Hausa, har wasun su yanzu sun shiga kiristanci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun Shehu yana yawon wa&#8217;azi tsakanin masarautun Gobir da Zamfara da Kabi, kafin maganar jihadi ta taso, ya muhimmantar da musuluntar da maguzawa. Shi ya sa daga cikin matakan da Sarkin Gobir Yunfa ya dauka na kokarin dakile da&#8217;awar Shehu shine ya yi dokar cewar ya haramta wa duk wanda ko dama shi ba musulmi ba ne shiga musulunci a hannun Shehu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tajdidin Shehu ba cikin kasar Hausa ne kawai ya yi sanadiyyar yaduwar musulunci ba. Sakamakon wannan Tajdidi ne musulunci ya yalwata ya karfafa a kasashen Nupe da Gwari da Yawuri (Kambari) da Zuru da Ilorin da sauransu. Daga baya kuma jikan Shehu, Sir Ahmadu Bello ya yi kokari tukuru wurin ganin cewar musulunci ya yadu ya karfafa a cikin kasashen Igala da Ebira da Plateau da kabilun Jihar Nasarawa da na Jihar Bauchi da Barno da Gombe da sauransu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sakamakon Tajdidin Shehu ne ya zama a yau Musulmi su suka fi yawa a arewacin Najeriya, har ake cewa Arewa ta musulmi ce.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da wannan kishin Addini ne da yiwa musulunci hidima ya kamata Musulmi ya auna Tajdidin Shehu Dan Fodiyo, ba da tsukakken tunani irin na kabilanci ko munana zato ba. Sai fa idan mutum ba musulmi ne ba, ko kuma yanzu Addini bai sha mashi kai ba, to wannan sai muce wasu manufofi daban gareshi na kawo fitinar kabilanci a arewacin Najeriya domin ya yaki musulunci karkashin rigar kabilanci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Modibbon Gusau.<\/p>\n<p>18\/11\/1446H<\/p>\n<p>16\/05\/2025M.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO &#8211; TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (5). &nbsp; A . GABA TA FARKO: AMSAR TAMBAYA TA FARKO TA MANHAJAR TATTAUNAWA (2): &nbsp; TASIRI DA AMFANIN TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO A KASAR HAUSA DA AREWACIN NAJERIYA A ADDINANCE DA SIYASANCE DA ABUNDA YA SHAFI YANAYIN ZAMANTAKEWA DA TATTALIN ARZIKI. &nbsp; [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4521,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[62],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4533","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-books-journal"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4533","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4533"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4533\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4534,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4533\/revisions\/4534"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4521"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4533"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4533"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4533"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}